Malamai 207 da aka dakatar a Jihar Zamfara, sakamakon sakaci da aiki da kuma masu dalilai sun mika takardar neman afuwa ga gwamnatin jihar, ta hannun kwamishinan ilimi da kimiya, Hon Wadatau Madawaki.
Idan dai za a iya tunawa, a watan satumbar shekarar da ta gabata ce gwamnatin Jihar Zamfara ta gudanar da tantance ma’aikatan bogi, da wadanda ke aiki biyu da kuma wadanda ba su zuwa aiki har takai ga dakatar da malaman makarantun sakandire guda 207.
- An Cafke Wadanda Ake Zargi Da Daba Wa Dan Wasan Nijeriya Mazaunin Kasar Ireland Wuka Har Lahira
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [8]
Dangane da haka ne ma’aikatan da aka dakatar sun amsa da kura -kiransu tare da mika uzurinsu a rubuce ga kwamishinan ilimi na jihar domin mika wuya ga gwamnan jihar.
A madadin sauran malamai da abin ya shafa, Nafisa Isah da Danlami Lawal sun yi jawabi a lokacin da suke gabatar da neman afuwa tare da daukar alkawarin ba za su sake maimaita kuskuransu ba.
Da yake jawabi bayan amsar takarar neman afuwan, kwamishinan ilimi da kilmiya, Hon Wadatau ya bayyana cewa, kwamitin tantance malaman ya yi iyaka bakin kokarinsa wajen zakulo da malam bogi da wadanda ba su zuwa aiki, sannan ku kasansu malaman da abun ya shafa sun tabbatar da cewa sun yi babban kuskure wanda suka nemi afuwa ga gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal.
Ya ce za a mika wa gwamna wannan takarda tasu domin yin afuwa da su koma aikinsu idan har gwamnan ya amince. Ya ce gwamna mai tausai ne kuma yana mai tabbacin zai yafe masu domin su koma bakin aikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp