Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT), reshen Babban Birnin Tarayya, ta sanar da janye yajin aikin da malaman makarantun firamare suka fara tun ranar 24 ga watan Maris, 2025.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne bayan wani taron shugabanni da suka yi a ranar 4 ga watan Yuli, 2025, sannan aka fitar da sanarwar ranar Talata, 8 ga watan Yuli, 2025.
- Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
- Babatun Lai Ching-Te Ba Zai Taba Girgiza Kasancewar Sin Day Tak A Duniya Ba
NUT ta umarci dukkanin malamai na makarantun firamare a Abuja da su koma bakin aiki a ranar Laraba, 9 ga watan Yuli, 2025.
Sun janye yajin aikin ne bayan Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayar da umarnin sakin Naira biliyan 16 domin biyan wani kaso daga cikin albashin da malaman ke bi.
Ƙungiyar ta gode wa malamai bisa juriya, haÉ—in kai da addu’o’in da suka yi a lokacin da suke gudanar da yajin aikin da ya É—auki watanni huÉ—u.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp