Shugaban kungiyar Malaman jami’oi reshen jami’ar Ilorin (ASUU) Dakta Aled Akanm ya bayyana cewa wasu daga cikin Malaman jami’oin sun zama direbobin motocin Uber da kuma mabarata saboda irin yanayin rayuwar da suke fuskanta,hakan kuma ya samo asali ne kan yadda tsarin aikin nasu yake.
Ya kara wasu daga cikin Malaman jami’oin sun zama mabarata ne ba domin komai ba sai saboda su samu damar yadda za su tafiyara da rayuwar iyalansu.
- Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63
- Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya
Da yake jawabi lokacin da ayke ganawa da jaridar LEADERSHIP ta ranar Lahadi a makon da ya gabat a Ilori, hakanma akwai Malaman jami’oin da suke karbar bashi domin su samu tafiyar da rayuwarsu kamar yadda ya kamata.
“Maganar gaskiya ce mambobinmu suna fuskantar matsananciyar rayuwa a halin da ake ciki yanzu. Wadanda bsu da lafiya ba za su iya ci gaba da lamarin na kula da lafiyarsu.Da yake darajar Naira ta yi kasa sosai yayin da kuma dala sama take kara yi, sau da yawa shi albashin ba wani abin azo a gani bane. Mutane suna rayuwa ne akan bashi, hanyar adashin hadin gwiwa na ma’aikata, sai kuma roko, ko kuma samun kudi ta hnyar noma, da hanyar tuka mota taUber, ko kuma ta taimakon ‘yan’uwa idan har abin ya kai ga ta’azzara.
“Al’amarin ya kai ga kaiwa bango domin uanzu Malaman makaranta suna kwana a ofisoshinsu,ko su bar motar motocinsu,su shiga mota haya, ko kuma wani lokaci su yi tafiya a kasa wani lokaci mai tsawo domin su rage yawan kudin motar da za su biya cewar Akanmu,”.
Da yake kara nuna damuwarsa ya ce albashi Malaman jami’oi ya tsaya hakanan ba gaba bare bayam a tsawon shekaru 16 da suka gabata, cewar Akanmu,“Wannan rashin daukar mataki akan matsalolin shi yasa suke fuskantar manyan matsaloli, bama idan aka danganta su takwarorinsu na ksashen duniya. Yana da kyau a gane cewa kungiyar ASUU ba ta manta bane da duk irin yarjejeniyoyin da aka yi da gwamnatin tarayya, wadand a har yanzu basu haifar da da mai ido ba,domin kuwa kusan duk yarjejeniyoyin da aka yi dasu babu wadanda suka aiwatar.”
Ya yi kra da gwamnatin tarayya ta yi wani abu akan yarjejeniyar da aka yi da ita a shekarar 2009, ba Jami’oi isassun kudade su/ gyara jami’o, Jami’oi su tsaya da kansu,karin albashi kashi 25 zuwa 35, na karin albashi na ariyas na shekara hudu rashin biyan wasu ,alawu- alawus na Ma’aikatan jami’oi.
Ya ce, “Yarjejeniya ta maida hankali ne kan kudaden da za’a ba jami’oi za’a biya cikin shekaru da suka kai har Naira Tiriliyan 1.5, samar da kayan koyarwa da kuma yin bincike.
“Maganar alawus alawus kamar yadda aka amince a sahu na uku da hudu na yarjejeniyar yadda Akanmu ya kara jaddadawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp