Malamar jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Dakta Comfort Adokwe, da aka yi garkuwa da ita, ta kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan shafe kwanaki uku a hannunsu.
Dakta Adokwe dai ta samu kubuta ne a daren ranar Talata bayan biyan kudin fansa naira miliyan biyar da iyalanta suka biya, kamar yadda wakilinmu ya gano a ranar Laraba.
- Tinubu Ya Nada Kwamishinonin INEC A Jihohi 9
- UNESCO Ta Yi Bikin Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yada Bayanai Ta Duniya A Abuja
Idan za a tuna, Dakta Adokwe, wacce malama ce a tsangayar nazarin mulki kuma mataimakiyar daraktan darusan jinsi, an yi garkuwa da ita ne a gidanta da ke Angwan Jaba a cikin garin Keffi a daren ranar Lahadi.
An nakalto cewa ‘yan bindigan sun yi ta harbe-harbe a sama lokacin da suka je gidan matar daga bisani suka yi awun gaba da ita.
LEADERSHIP tun da farko ta labarto cewa masu garkuwan sun nemi kudin fansa naira miliyan 15 kafin su sake ta, amma iyalanta sun nuna cewa wannan kudin ya musu yawa ba za su iya biyan hakan ba.
Daya daga cikin iyalanta, Mista Timothy Adokwe, ya shaida wa ‘yan jarida cewar an sako malamar da karfe 10 na daren ranar Talata bayan da aka biya kudin fansa.
Ya ce, daya daga cikin ahlin malamar ne ya kai kudin zuwa inda masu garkuwan suka umarta daga bisani suka sako ta.
Ya kara da cewa hukumomin tsaro sun yi iyaka nasu kokarin wajen bibiyar masu garkuwan, amma an dakile aniyarsu domin tabbatar da cewa ba a jefa rayuwar malamar cikin hadari ba.
“Mun fi damuwa kan yadda za mu kare ‘yar uwanmu. Jami’an tsaro sun yi iyaka kokarinsu, sun taimaka wajen bibiyar sawun masu garkuwan.
“Amma bisa gargadin da masu garkuwan suka yi na cewa muddin aka yi wani motsi to za su kasheta, hakan ya sa muka roki jami’an tsaron da kada su yi wani abu domin tabbatar da lafiyarta.
“Ina sane da cewa hukumomin tsaron sun bibiya dukkanin abubuwan da suka faru kila za su bibiyi sawun masu garkuwan.
“Muna godiya wa kowa da kowa bisa taimako har zuwa lokacin dawowar ‘yar uwan namu,” ya shaida.