Hukumar Hisba ta jihar Kano na binciken wani malamin Islamiyya da ake zargi da yin lalata da daliban makarantar mahaifinsa da ya rasu a jihar.
Aminiya ta rahoto daga Freedom Rediyo cewa kazantar lamarin ta kai ga har malamin Islamiyyar ya dirka wa guda daga cikin daliban nasa ciki.
Makarantar Islamiyyar dai fitacciya ce a unguwar Nassarawa da ke Kano, kuma mallakin wani malami da yi fice wajen hidimta wa addinin Musulunci a jihar ne, wanda bayan rasuwarsa ’ya’yansa suka dauki ragamar koyarwar.
Aminiya ta kara da cewa, bayan bullar cikin da malamin ya dirka wa guda daga cikin daliban nasa, ya aure ta; Inda suka hada kai da ita matar ta shi, tana jawo masa dalibai gidansu na aure, yana lalata da su.
Malamin Islamiyyar ya shiga hannun Hisba ne bayan an tsegunta mata yadda yake amfani da matsyinsa yana lalata da dalibansa mata.
Bayanai sun nuna wanda ake zargin yana nuna wa daliban cewa soyayya kawai yake son yi da su, idan suka amince kuma a hankali ya fito musu da bukatarsa.
Shugaban Hukumar Hisba Muhammad Harun Ibn Sina ya ce wata majiya ce ta tsegunta musu lamarin, kuma a binciken da suka fara gudanar wa sun gano akwai kamshin gaskiya a zarge-zargen.