Manchester City ta kai wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan da ta doke Real Madrid da ci 4-0 a daren Laraba.
An dai buga wasan ne a filin wasa na Etihad, inda aka tashi wasan farko na wasan kusa da na karshe da ci 1-1 a babban birnin Spaniya kwanaki takwas da suka gabata.
A mintuna 45 din farko, dan wasan Man City, Bernardo Silva ya zura wa Madrid kwallaye biyu a raga.
Daga can City bata waiwaya ba a zagaye na biyu, ta ci gaba da tasa keyar Real Madrid har sai da mai tsaron gidanta, Militao ya ci gida daga bisani kuma a mintunan karshe Julian Alvarez ya sake zura kwallo ta hudu.
Ana fatan City za ta lashe kofin Premier da gasar zakarun Turai da kofin FA – kamar yadda Manchester United ta yi a 1999.
City za ta kara da Inter Milan a wasan karshe da za a yi a Istanbul a ranar 10 ga watan Yuni bayan da kungiyar ta Italiya ta lallasa AC Milan a gida da ci 2-0 a wasan farko sannan ta sake lallasata da ci 0:1 a wasan kusa da na karshe.