Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta fara kakar wasa ta bana da kafar dama a kokarin da take yi na ganin ta Kuma lashe gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Kwallon farko ta sabuwar kakar Firimiya Manchester City ta casa Burnley wadda ta samu damar buga gasar bayan lashe kofin ‘yan dagaji.
- Gwamnatin Kano Ta Kammala Tsara Tunkarar Matsalar Ambaliyar Ruwa
- Gwamnatin Gombe Za Ta Dauki Sababbin Ma’aikatan Lafiya 200
Erling Haaland ne ya fara jefa kwallo minti uku kacal da fara wasan kafin ya kara a minti na 34.
Bayan dawowa hutun Rabin lokaci Rodri UA jefa ta uku Kuma ta karshe yayinda City ta fara teburin Firimiya.