Manchester City a ranar Laraba ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Sevilla Fc ta kasar Sifen.
Inda ta lashe kofin Super Cup da aka buga a kasar Girka.
Sevilla ce ta fara jefa kwallo ta hannun Yusef En Nesyri a minti na 25 kafin matashin dan wasan city Cole Palmer ya farke kwallon.
Da haka ne wasan ya tashi sai aka tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga inda dan kwallon Sevilla Gudelj ya barar da Kwallon da ya buga wanda ya baiwa city damar lashe gasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp