Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nuna sha’awar daukar dan wasan gaban Wolves Matheus Cunha a wannan bazarar, Cunha dan wasan kasar Brazil yanzu haka yanada kwantiragin fam miliyan 62.5 a Wolves, ana sa ran zai bar Molineux a karshen kakar wasa ta bana.
Majiyoyi da dama sun shaida wa BBC cewa dan wasan mai shekaru 25 na daya daga cikin jerin zabukan yan wasan gaba na gefe da United ke nema tare da dan wasan gaban Ipswich Town Liam Delap, mai shekara 22, shi ma kungiyar ta Old Trafford na zawarcinsa.
- Nda-Isaiah Ta Yaba Wa Matar Shugaban Kasa Tinubu Kan Soyayya Da Tallafawa Talakawan Nijeriya
- Yadda Aka Yi Zanga-zanga Kan Matsalar Tsaro A Filato
Kocin Manchester United Ruben Amorim na fatan ganin ya bai wa zura kwallaye fifiko a wannan kakar sakamakon kanfar kwallaye da kungiyar ke yi, Southampton, Leicester City, Ipswich, Everton da kuma West Ham ne kawai suka zura kwallaye kasa da kwallaye 38 da United ta ci a wasanni 33 na gasar Firimiyar bana.
Ana kallon Cunha a matsayin wani da zai iya bayar da gudunmawa wajen dawo da Manchester United kan ganiyarta, Cunha ya kasance wanda ya fi zurawa Wolverhampton kwallaye a raga a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 16 a dukkanin gasa.
United na shirin fuskantar gogayya daga kungiyoyi da dama na gasar Firimiya kan Cunha, inda Liverpool, Arsenal, Chelsea da Newcastle duk sun kasance suna zawarcin dan wasan gaban a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp