Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta sanar da makomar dan wasan ta Mason Greenwood kafin a fara kakar wasa ta shekara ta 2023 zuwa 2024 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Manchester United za ta fara wasan farko a Premier League da fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Wolberhampton ranar 14 ga watan Agusta kamar yadda hukumar shirya gasar ta tsara tun farko. Ranar 2 ga watan Fabrairu an soke zarge-zargen da ake yi wa Greenwood,
- Na Fi So Na Fito A Masifaffiya -Amina Miloniya
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Masallacin Juma’a A Zamfara
ciki har da laifin fyade, sai dai masu shigar da kara sun ce shaidu sun janye bayar da shaida, sannan an samu haske kan lamarin zargin da ake yi masa da ta kai aka soke su.
Sai dai Manchester United ta sanar da cewar ta fara nata binciken dan kwallon kan laifin da aka zarge shi amma tun daga lokacin da aka fara zargin Greenword, bai sake buga wa Manchester United wasa ba, kuma yana da kwantiragin da zai kare a Old Trafford a karshen Yunin shekara ta 2025.
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Erik Ten Hag ya sanar cewar ya bayar da shawarar da ya kamata a dauka kan dan wasan, amma ya kara da cewar kungiya ce za ta yanke hukunci na karshe. Wasu na cewar Manchester United ta yanke hukunci kan makomar dan kwallon, wadda za ta sanar da hukuncin da ta dauka kafin ta kara da Wolberhampton a cikin wannan watan.