Manchester United na shirin biyan fam miliyan 60 domin ɗouko ɗan wasan gaban Brentford, Bryan Mbeumo.
A baya, United ta tura tayin fam miliyan 45 amma Brentford ta ƙi amincewa.
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3
- Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
Yanzu ana ci gaba da tattaunawa domin yiwuwar ɗaukarsa, kuma idan ya zo, zai zama ɗan wasa na biyu da United ta ɗauka a bana.
Tun bayan da Manchester United ta ɗauki Matheus Cunha daga Wolves a kan kuɗi Yuro miliyan 62.5, kulob ɗin na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa gaban ‘yan wasanta kafin su fara atisaye a ranar 7 ga watan Yuli.
Sabon kocin Tottenham, Thomas Frank, yana sha’awar haɗuwa da Mbeumo a kulob ɗinsa.
Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan.
Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi.
Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka aka zura wasu tara.
Sai dai akwai yiwuwar shi da abokin wasansa na tawagar Kamaru, Andre Onana, ba za su buga wasannin farko na sabuwar kakar wasa ba saboda za su wakilci Kamaru a gasar cin kofin ƙasashen Afirka da za a buga a Maroko.
Kamaru za ta fara buga wasa da Gabon ranar 24 ga watan Disamban 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp