Manoma sama da dubu 10 ne za su ci moriyar sabon shirin bunkasa noman rani a Sokoto wanda aka bayar da aikinsa kan naira biliyan 3.4.
Shugaban Karamar Hukumar Kware, Honarabul Jafaru Hamza ne ya bayyana hakan a yau ga tawagar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Sakkwato a ziyarar gani da ido da suka kai a ayyukan da Gwamnatin Tambuwal ta aiwatar a Kware.
“Wannan shirin wanda aikinsa ya kai kashi 90 cikin 100 zai bunkasa noman rani sosai, akalla sama da manoma 10, 000 za su ci moriya, aiki ne wanda zai habaka samar da abinci a ciki da wajen Jiha, haka ma zai bunkasa haraji da karuwar tattalin arziki.” Ya bayyana.
Honarabul Jafaru wanda ya bayyana cewar shirin bunkasa noman rani na Kware da za a kammala a Disamba, hadakar shiri ne tsakanin Gwamnatin Sakkwato, Gwamnatin Tarayya da kuma Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, ya ce shirin zai rika samar da shinkafa ga sabon kamfanin Shinkafa na Dangote da za a kammala a Karamar Hukumar.
Ya ce tun zamanin Firmiyan Yankin Arewa, Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato aka assasa shirin noman rani a Kware amma sama da shekaru 30 wajen ba ya aiki, wanda akan hakan ne Gwamnatin Tambuwal ta yi hobbasar kwazon raya aikin noma a wajen.
Ya ce a yanzu haka an gyara kadada 450 cikin 800 da ke akwai, haka ma za su rika samun ruwa ne daga tafkin Rima da na Kalmalo, haka ma an dauki kwararan matakan kiyaye ambaliyar ruwa.
Shugaban wanda ya zagaya da ‘yan Kungiyar a wuraren mabambantan ayyuka ya bayyana cewar “Kun ga sabuwar Babbar Asibitin Kware wadda aka bude a shekarar da ta gabata kuma ta na aiki yadda ya kamata, kun kuma ga sabon gidan ruwa mai daukar lita miliyan 1.5 da sabon ofishin ‘yan Sanda da makarantu, hanyoyin mota da sauransu. Bakidaya Gwamnatin Tambuwal daga 2015 zuwa yau ta aiwatar da ayyuka sama da 200 a Kware wadanda suka yi matukar tasiri ga al’umma.” In ji shi.