Bayan yarjejeniyar da kasashen Sin da Kenya suka rattabawa hannu dangane da shigar da Avocadon Kenya zuwa kasuwar kasar Sin a watan Janairun bana, kashi na farko na Avocadon ya shigo cikin watan Augustan da ya gabata, kuma tuni ya fara samun karbuwa.
Zola Franco, dan asalin kasar Mexico dake da dakin cin abinci a birnin Tianjin na kasar Sin, yanzu ya sauya Avocadon Mexico, wadda ita ce kan gaba wajen nomansa a duniya, da na kasar Kenya a cikin wasu girke-girkensa da suka yi fice.
Haka kuma, Avocadon manomin kasar Kenya Richard Tuwei, sun riga sun iso kasar Sin har ma an sayar da su kan farashi mai rahusa.
Richard Tuwei na daya daga cikin manoma na farko da suka fara fitar da Avacado ta jirgin ruwa zuwa kasuwar kasar Sin.
Hukumomi a kasar Kenya sun ce za a rika kara yawan Avocadon da za a kawo kasar Sin a hankali zuwa ton 100,000 a kowacce shekara, cikin shekaru kalilan masu zuwa.
A matsayinta na kasa ta biyu da ke shigo da amfanin gona daga kasashen Afrika, yawan karuwar kayayyakin dake zuwa kasar Sin ya kai kaso 11.4 a shekarun baya-bayan nan.
A shekarar 2021, yawan amfanin gona daga nahiyar Afrika da ya shigo kasar Sin, ya karu da kaso 18.2. (Fa’iza Mustapha)