Kwanan baya, taron majalisar ministocin kasar Nepal, ya yanke shawarar dakatar da hada gwiwa tare da kasar Amurka, kan wani shirin da ake kira SPP, ko kuma shirin dangantakar abokantaka tsakanin jihohi.
Kafafen yada labaran kasar Nepal sun ruwaito cewa, tun a shekara ta 2015, sau da yawa Amurka ta bukaci Nepal ta shiga shirin SPP, amma Nepal din ba ta yarda ba, saboda damuwar ta kan kulla kawancen soja da Amurka.
Daftarin shirin SPP tsakanin Nepal da Amurka, na kunshe da abubuwa da yawa, ciki har da kaddamar da atisayen soja a yankin filato na Nepal, sa’annan rundunar tsaro ta Amurka, za ta iya shiga cikin Nepal ba tare da wani tsaiko ba, kana, Amurka za ta samar da bayanan sirri na yaki da ta’addanci, da na’urorin aikin soja ga Nepal da sauransu. Abun lura a nan shi ne, duk wadannan abubuwa na da alaka da aikin soja, kana, tamkar shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan Nepal.
Kasar Nepal na bakin iyaka da kasashen Sin da Indiya, inda a ‘yan shekarun nan, kasar Amurka take kara aiwatar da manufarta game da yankin tekun Indiya da Pasifik, a wani yunkuri na shigar da Nepal a ciki.
Hakikanin gaskiya, irin abun da Amurka ta yi a Nepal, shi ne yunkurin shawo kan kasar Sin. Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya yi jawabin cewa, ya kamata a “gina” muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen kasar Sin. Makasudin bangaren Amurka a zahiri shi ne, kawo cikas ga ci gaban kasar Sin.
Amma irin abun da Nepal ta yi a wannan karo, yana kawo tsaiko ga manufar Amurka, kana hakan masomi ne kawai.
Ko shakka babu, manufar Amurka game da yankin tekun Indiya da Pasifik da take kokarin yayatawa, ba za ta yi nasara ba. (Murtala Zhang)