Jiya ne, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takarda ta hakika mai taken “karya kan ra’ayin Amurka game da kasar Sin”, inda ta fallasa “yadda yaudara, munafunci da hadarin dake kunshe cikin manufofin Amurka game da kasar Sin” tare da cikakkun bayanai da kuma alkaluma.
Dangane da batutuwa daban-daban da suka shafi kasashen biyu, takardar ta yi watsi da yadda kasar Amurka ta yi yunkurin mayar da kasar Sin saniyar ware ta hanyar yayata labarin wai “barazana” na kasar Sin, da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da kuma neman bata sunan manufofin gida da waje na kasar Sin.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)