Koyo wata hanya ce da ta kunshi yadda ake samun ilimi ta hanyoyi daban-daban na sadarwa ta yada labarai kamar karatu, sauraren wani abu da dai sauransu duk da yake ana amfani da al’amarin ta wasu hanyoyi daban,sai dai kuma koyo ba an takaita shi ba ne kan kalmar ilimi, maganar gaskiya abin ba an tsaida shi ga dan Adama kadai ba kadai. Har dabbobi ma ana koya masu domin su san wadansu dabaru, har mashin ma ana koya ma shi ya yi wasu ayyuka abubuwa. Abin ba ya tsaya kadai ba ne kan abubuwan da suke kawo matsala wajen koyon abin da suke bukatar koyo. Don haka shi koyo anan yana nufin koyon karatu da kuma rike abin da aka koya domin yin amfani da shi a gaba, inda abin zai iya kasancewa a bayyane.
Koyo wata hanya ce data kunshi duk abin da ya shafi wayewa kamar dai yadda muke zama a wuri muna koyon abubuwa kullun saboda zaman da muke yi tare da mutane, muna maida hankali, mu kalla, mu yi tunani kan al’amarin,mu ga yadda abin yake,da kuma timakawa wajen samo manufa kan abubuwan da aka lura da su lokacin koyon.
Abubuwan Da Suke Kawo Nakasu Wajen Koyo
Kamar yadda mutane suka bambanta hakanan ma yanayin fahimtarsu ta koyon karatu ta bambanta yana kuma da muhimmanci a gane abubuwan da suke kawo nakasu ga kokarin da ake yi na koyon karatu da gane abin da aka koya, wannan kuma ya bambanta daga wannan mutumin zuwa wancan.
Fahimtar Abin Da Ake Koyo
Wannan shi ne daya daga cikin abubuwan da suke kawo nakasu wajen harkar koyo domin kuwa mutane sun sha bamban, dangane da abin da suka fi ganewa a zuciyarsu.Wadansu fahimtarsu da gane abin da suka koya tafi dacewa da darasin lissafi wannan kuma shi zai nuna cewa ba za su samu matsala bai dan suka dauki mataki na yin nazarin al’amarin daya shafi bangaren kimiyya, yayin da wasu na iya fuskantar matsala akan darasin na lissafi.Bugu da kari wadanda suke samun matsala da lissafi sai sai darasin tattalin arziki da al’amarin da ya shafi dan Adam da sauki wajen ganewa.
Yana da matukar kyau koda yaushe a rika kula da irin yadda fahimtar mutum take akan abin da yake koyo, ko shi ya gane inda basirar ta shi take kafin ya kai ga yanke shawarar abin da zai zama ko yi a gaba a rayuwar shi koyo.
Idan kuma mutum ya san shi bai san irin abin da zai zama ba a gaba ko fannin da yake son ya karanta shawarar data kamata ita ce ya rubuta jarabawa saboda yin hakan ne za a iya ganewa irin abin da ya dace da shi a gaba, ba wai ya sa kan shi yin abin da shi ba zai iya ba. A tsarin ilimin shekarun baya da suka gabata idan mutum ya kawo kusa da karshen aji biyu na makarantar Sakandare zai rubuta jarabawa da ake kira da suna aptitude test,bayan an kammala gyaranta ne daga nan za a gane inda kowa ya dace a kai shi, ko darasin da ya dace ya yi. Wani za a mai da shi ajin da za a rika yin darussan kimiyya,wasu kuma a kai su makarantun koyon sana’a wato technical school,wasu a tura su makarantun horon Malamai yayin da wasu kuma makarantu koyon kasuwanci wato commercial college,wasu kuma a maida su azuzuwan da za a rika koya darussan da suka bambanta da na kimiyya. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.