Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da manyan ayyuka guda biyar, domin neman ci gaba da farfadowa tare, da kuma raya makomar al’umma ta bai daya. Masana sun bayyana cewa, jawabin da ya yi, ya kunshi shirin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, tare da ba da jagoranci kan aikin.
Ban da haka kuma, yayin taron na wannan karo, an zartar da “Sanarwar Beijing”, da “Shirin hadin gwiwa tsakanin shekarar 2025 zuwa ta 2027”, wadanda suka nuna aniyar Sin da Latin Amurka da Caribbean wajen karfafa hadin gwiwa, da fuskantar kalubaloli cikin hadin gwiwa.
Bisa jagorancin “manyan ayyuka guda biyar”, kasashen Sin da Latin Amurka da Caribbean za su neman ci gaba da farfadowa cikin hadin gwiwa, da raya makomar al’umma ta bai daya, tare da ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe maso tasowa gaba, ta yadda za a tabbatar da zaman karko, tare da samar da karfi ga kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp