Kwanan nan, gwamnatocin kasashe daban-daban, da manyan jami’ansu, gami da mutane daga sassan duniya, suna ci gaba da bayyana matsayinsu na goyon-bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da mara baya gami da mutunta kudiri mai lamba 2758 na babban taron Majalisar Dinkin Duniya, da kin yarda da duk wani yunkuri na ware Taiwan daga kasar Sin.
Shugaban kasar Afirka ta Tsakiya, Faustin-Archange Touadéra, ya ce yana goyon-bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ba zai sauya matsayinsa ba.
- Firaministan Sin Ya Sauka A Seoul Domin Halartar Taron Kasashen Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu
- Mun Ƙudiri Aniyar Ba Duk ‘Ya’yan Zamfara Ilimi – Gwamna Dauda Lawal
A nata bangaren kuma, shugabar majalisar dokokin kasar Malawi, Catherine Gotani Hara, ta sake jaddada cewa, kasarta na yin tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da mara mata baya wajen dunkule duk kasar baki daya, da kin yarda da duk wani yunkuri na balle Taiwan daga cikinta, kuma Malawi ba za ta sauya wannan matsayin ba.
Shi ma shugaban cibiyar nazarin tattaunawar kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu, Dr. Philani Mthembu ya bayyana cewa, yunkurin goyon-bayan ware Taiwan daga kasar Sin na tattare da hadarin gaske, kuma ya kamata jagororin yankin Taiwan, su yi aiki bisa nauyin da aka danka musu. (Murtala Zhang)