• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Jami’an Najeriya Na Amincewa Da Alfanun Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ga Kasashen Afrika

by CGTN Hausa
2 years ago
Afrika

A bana ake cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma a farkon watan Oktoba, na ziyarci Najeriya, wadda take daya daga wasu kasashen Afrika wadanda suka riga sauran kasashen duniya amincewar shawarar. Domin fahimtar amfanin shawarar ga kasar, na zanta da kakakin majalisar wakilai, da ministan harkokin wajen kasar.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Abbas Tajudeen ya ce, “Tashar teku ta Lekki da kamfanin CHEC ya gina, da layukan dogo, da sauran ayyukan da kamfanin CCECC ya gudanar, da ma yankin ciniki maras shinge na Lekki, da na Ougun da Guangdong da sauransu, ba ma kawai sun samar da dimbin guraben aikin yi ba ne, har ma sun ingiza bunkasuwar tattalin arziki ga al’ummar wurin.” Shawarar na amfanar al’ummar Najeriya matuka, kuma kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan shawarar, a cewar Abbas Tajudeen.

  • Kamfanonin Sadarwa Na Kenya Sun Yi Hadin Gwiwa Da Na Sin Don Kaddamar Da Kamfanin Hada Wayoyin Hannu
  • An Kammala Taron Tsaro Na Xiangshan Karo Na 10 Na Beijing

A nasa bangare kuwa, ministan harkokin wajen kasar Yusufu Tuggar cewa ya yi, “A matsayin kasa mai yawan jama’a kuma mafi karfin tattalin arziki a Afrika, shawarar ta dace da tsarin raya kasa. Kaza lika kasashen biyu suna hadin kai a fannin samar da manyan ababen more rayuwa, da horar da kwrarru, da dai sauran bangarori, ciki hadda tashar Lekki, da jirgin kasa dake Lagos, da layin dogon dake tsakanin Abuja da Kaduna, wanda ya kasance irinsa na farko a Afrika dake amfani da fasaha da ma’aunin Sin, da kuma sabon filin saukar jiragen sama na Abuja, wanda ya zama sabuwar alamar Abuja.

Ban da wannan kuma, na dawo nan kasar Sin a tsakiyar watan Oktoba, inda na zanta da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, wanda ya halarci taron kolin kasa da kasa na tattaunawar hadin kai bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3 a birnin Beijing, inda Shettima ya ce, shawarar na da babbar ma’ana ga bunkasuwar Afrika, wadda ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da manyan ababen more rayuwa a kasashen. Alal misali a Najeriya, layukan dogo da kasashen biyu suka yi hadin kai wajen ginawa na da amfani matuka ga kafa tsarin zirga-zirga a kasar, da raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a. Layin dogon tsakanin Abuja da Kaduna da aka riga ake amfani da shi na ingiza bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar Najeriya sosai. Ban da wannan kuma, Shettima ya ce, yayin zantawarsa da shugaban Sin Xi Jinping, sun kai ga matsaya daya, kan hadin kai a bangaren manyan ababen more rayuwa, kuma za a ci gaba da sa kaimi ga shimfida layukan dogo da dai sauran ayyuka a Najeriya.

Manyan jami’an Najeriya da dama suna amincewa da damammaki, da bunkasuwa da shawarar take kawowa kasashen Afirka, musamman ma Najeriya. A ganinsu, shawarar na taka rawa wajen raya manyan ababen more rayuwa, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da daga karfin takarar kasarsu, har ma da samar da makoma mai haske a fannin hadin kai da cin moriya tare a nan gaba.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Ci gaban da Najeirya ke samu bayan ta shiga wannan shawara, ta zama misali ga amfanin shawarar ga Afrika har ma ga dukkanin fadin duniya. An yi imanin cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, karin kasashe musamman ma kasashen Afrika, za su amince da wannan shawara da za su shiga, don more damammakin shawarar, da kuma kara amincewa tsakanin Sin da kasashen Afrika a bangaren siyasa, da al’adu, da hadin kan tattalin arziki, har ma ta kai ga taka rawa wajen samun zaman lafiya da karko a duniya baki daya. (Mai rubuta: Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Sin

An Mai Da Hankali Kan Ci Gaba Mai Inganci Yayin Taron Koli Kan Harkokin Kudi Na Sin

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Afrika

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.