ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Jami’an Sin Da Amurka Sun Yi Shawarwari A Lardin Hebei Na Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana jiya Litinin cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya yi shawarwari da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasifik Daniel Kritenbrink, da babbar darekta mai kula da harkokin kasar Sin a majalisar tsaron Amurka Laura Rosenberger, ranar 11 da 12 ga watan Disamba a lardin Hebei dake arewacin kasar Sin. 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi, kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a watan da ya gabata a birnin Bali na kasar Indonesia.

  • Kasar Sin Ta Amsa Sunanta Na Aminiya Ta Kwarai Ga Kasashen Afrika

Wang ya ce, bangarorin biyu sun kuma tattauna kan ci gaba da tuntubar juna, kan ka’idojin Sin da Amurka, da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, kamar batun yankin Taiwan, da karfafa mu’amala a dukkan matakai, da hadin gwiwa a wasu fannoni.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, sun yi musayar ra’ayoyi da dama kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya masu muhimmanci dake shafar muradunsu na bai daya, in ji kakakin, inda ya kara da cewa, bangarorin biyu sun amince cewa, tattaunawar ta gaskiya ce, mai zurfi da kuma inganci, kuma za su ci gaba da tuntubar juna.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar na nuna cewa, ziyarar za ta share fagen ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kawo kasar Sin a farkon shekarar 2023. (Ibrahim Yaya)

LABARAI MASU NASABA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
Next Post
An Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja Saboda Bukukuwan Karshen Shekara

An Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja Saboda Bukukuwan Karshen Shekara

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

November 17, 2025
Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

November 17, 2025
Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

November 17, 2025
Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

November 17, 2025
Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.