• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
4 days ago
INEC

Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan zai fuskanci wasu manyan kalubale a shugabancin hukumar, yayin da ya gada tsarin zabe da ke cike da cece-kuce, rashin amincewar masu jefa kuri’a, da matsin lamba na tabbatar da cewa an gudanar da zabe mai inganci.

 

An nada shi ne bayan amincewar majalisar zartarwa ta tarayya a lokacin zaman majalisar wanda ya gudana a Abuja ranar Alhamis da ta gabata. Ya dai kasance dan asalin Jihar Kogi ne da ke arewa ta tsakiya.

  • Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja
  • 2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Ya dai gaje Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa na shekaru 10 ya kare a matsayin shugaban INEC a ranar Talata.

 

LABARAI MASU NASABA

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa.

 

Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya ce tarihin Amupitan na ciki da kwazo da adalci da kwarewa da hidimar kasa.

 

Bayan amincewar majalisar, ana sa ran shugaba zai mika sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa don tantancewa da tabbatarwa bisa ga tsarin kundin mulkin Nijeriya.

 

Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, dan asalin kauyen Ayetoro Gbede a cikin karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Ya kasance farfesa ne a bangaren shari’a a jami’ar Jos ta Jihar Filato, shi ne mataimakin shugaban jami’a. Haka kuma, shi ne shugaban kwamitin majalisar gudanarwa na jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun.

 

Jam’iyyun siyasa sun yi kira ga Farfesa Amupitan da ya dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaben Nijeriya ta hanyar gaskiya, rashin son zuciya, da gyara tsarin hukumar.

 

A martani jam’iyyar hadaka ta ADC ta gargadi sabon shugaban INEC, da ya kasance mai biyayya ga mutanen Nijeriya ba wai ga bukatun siyasa ba. Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyar PDP ta yi kira gare shi da ya fifita tsarkake tsarin zabe ta hanyar sauye-sauye domin dawo da amincewar jama’a ga hukumar.

 

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta nuna gamsuwa da nadin Amupitan, inda ta bayyana cewa an zabe shi ne bisa cancanta kuma dole ne ya nuna adalci, gaskiya, da himma wajen ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren zabe da ake yi.

 

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, sakataran yada labarai na kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi kira ga sabon shugaban INEC da ya sanya aminci ga mutanen Nijeriya maimakon na gwamnatin APC mai mulki. Abdullahi ya jaddada bukatar dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaben kasa, yana mai cewa jam’iyyar hadaka ta shirya bai wa sabon shugaban INEC hadin kai. Jam’iyyar tana fatan Amupitan zai yi aiki mafi kyau a zaben 2027.

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban matasa na kasa na jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya yi kira ga Amupitan da ya aiwatar da gyare-gyare da za su karfafa dimokuradiyyar Nijeriya.

A bangarensa, darakta halda da jama’a na APC, Bala Ibrahim, ya yaba da nadin, inda ya bayyana cewa nadin Farfesa Amupitan ya dogara ne kan cancanta.

Sai dai kuma ‘yan adawa sun kafa wa sabon shugaban INEC sharudda kan gyaran zabe da gaskiya da bin doka yayin da ya shiga ofisi.

A martaninsa kan nada Amupitan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, da jam’iyyar NNPP sun yi fatan alheri tare yin kira a gare shi ya yi taka tsantsan kan nadin da aka yi masa.

Sakataren yada labarai na kasa na Jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya yi kira ga Amupitan da ya gina jagorancinsa a kan bin doka kuma ya dauki darasi daga kurakuran da aka samu a zaben 2023.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Jonathan
Tambarin Dimokuradiyya

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

October 10, 2025
Next Post
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025
Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.