• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Kasashen Duniya Na Neman Cin Gajiyar Ci Gaban Kasar Sin

by CMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

A farkon wannan mako ne ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani ya fara ziyara a kasar Sin. Ziyarar da ta zo a daidai lokacin da ake ta tsokaci game da kasancewar kasar cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kasancewarta kasar Turai tilo dake cikin shawarar.

Yayin da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ke cika shekaru 10, kasar Italiya ta kasance cikin wadanda suka ci gajiyarta. Misali kadan daga ciki ya hada da yadda yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu ya habaka zuwa kusan dala biliyan 80 daga dala biliyan 50.

  • Kamfanin Makamashi Na Sin Ya Cimma Gagarumar Nasara A Fannin Karfin Wutar Lantarki Da Ake Iya Sabuntawa

Haka kuma yawan kayayyakin da Italiya ke shigo da su kasar Sin ya karu da kaso 30 cikin shekaru 5 da suka gabata. Wannan kadai ya nuna yadda Sin take taka gagarumar rawa wajen bunkasa cinikayya da ma tattalin arzikin kasar ta Turai. Haka zalika, ya nuna cewa, duk da yunkurin da wasu kasashen yamma ke yi na neman raba gari da Sin ko rage dogaro da ita, ra’ayin wasu da dama ya bambanta, kuma sun san abun da kasashensu da duniya ke bukata domin samun ci gaba a wannan zamani da ake fuskantar kalubale. Za mu iya gane hakan idan muka yi la’akari da cewa, Antonio Tajani shi ne babban jami’i na 4 daga kasashen kungiyar G7 da ya kawo ziyara Sin a baya-bayan nan.

Irin wannan ziyara da manyan jami’an manyan kasashe ke kawowa kasar Sin, yana kara bayyanawa al’ummar duniya cewa, jita-jitar da ake yadawa ba su da kamshin gaskiya ko kadan, kana ana yinsu ne da zummar bata sunan kasar Sin da kuma kokarin dakile ci gabanta, ganin irin tagomashin da take samu a duniya da ma jajircewarta wajen raya kanta bisa tsayawa da kafarta.

A yayin tattaunawarsa da ’yan kasuwar kasarsa dake Sin, Tajani ya ce gwamnatinsu na son inganta musu hanyoyin kara shiga kasuwar kasar Sin. Abun nufi, gwamnatin kasarsa na son kara cin gajiyar kasar Sin da ma dimbin damarmakin kasuwanci da bude kofar da take kara yi ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen ketare. Lamarin dake kara jaddada cewa, raba gari da kasar Sin ba abu ne mai yiwuwa ba. Kana su ma manyan kasashen duniya, suna son cin gajiyar ci gaban kasar Sin da dimbin damarmakin da take da su.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Ita dai Sin ta sha nanata cewa, a shirye take ta yayata fasahohinta tare da ba kasashen duniya damar cin gajiyar ci gabanta da tafarkin da ta dauka na zamanintar da kanta. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Next Post
Red Cross

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabar Kwamitin Kasa Da Kasa Na Red Cross

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.