Kwamitin haɗakar (JAC) na ƙungiyar malamai da waɗanda ba malamai ba na manyan makarantu mallakin gwamnatin jihar Bauchi sun shelanta tafiya yajin aikin sai babaa ta gani wanda hakan zai kai ga kulle makarantu baki ɗaya bisa rashin aiwatar musu da sabon tsarin biyan albashi na dukkanin ma’aikatan manyan makarantu wato (CONPCASS da CONTEDISS).
Shugaban kwamitin JAC, Kwamared Abubakar Ahmed wanda ya karanta jawabin bayan taron gaggawa da suka gudanar a ofishin ASUP da ke kwalejin ATAP ranar Litinin, ya ce, yajin aikin zai kai har a kulle makarantun dukka zai fara ne daga ranar Alhamis 2 ga watan Janairun 2025.
- NDLEA Ta Kama Mutum 415, Ta Kwace Tan 1.2 Na Kwayoyi A Bauchi
- Kirsimeti: ‘Yansanda Sun Kama Mutane 15 Da Ake Zargi Da Laifin Sata A Bauchi
A cewarsa, sun ɗauki wannan matsayar ne biyo bayan rashin gamsuwa da irin amsar da suka samu daga wakilan gwamnatin jihar da kuma irin nuna rashin damuwa da suka yi da buƙatun ƙungiyar a yayin zaman sulhu da suka yi a tare.
Kwamared Abubakar ya ce sun kuma cimma matsayar ne bayan ƙarewar wa’adin mako biyu da suka bayar wa gwamanti na yajin aikin gargaɗi da suka yi daga ranar 16 zuwa 30 na watan Disamban 2024 ba tare da samun wani sakamakon mai kyau daga wakilan gwamnati ba.
Makarantun da suke ƙarƙashin JAC ɗin sun haɗa da kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi da kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa, Kangere da Kwalejin ilimi da nazarin ilimin Shari’a da karatun komai da ruwanka ta A.D Rufai da ke Misau da kwalejin ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare da kwalejin ilimin harkokin noma da ke Bauchi da kwalejin horas da nasu da ungomaza ta Bill and Melinda Gates da ke Ningi.
Kwamitin ya nuna damuwarsa kan yadda wakilan da gwamnatin ta turo suke ƙoƙarin kawo naƙasu ga azamar gwamnan jihar na kyautata harkokin ilimi a manyan makarantun jihar, inda suka nemi a gaggauta aiwatar da sabon tsarin albashi kamar yadda yake ƙunshe a tsarin CONPCASS da CONTEDISS.
Injiniya Abubakar Ahmed ya nuna damuwa kan yadda ake barazana ga jagororin JAC da mambobinsu a faɗin makarantun bisa yadda suke tsayuwar daka wajen ganin an biya musu buƙatunsu. Sai ya nemi iyaye da dalibai da su yi haƙuri da zarar komai ya daidaita za su koma bakin aikinsu yadda ya kamata.
Kana sun yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi Bala Muhammad da ya tashi tsaye ya bibiyi lamarin domin gudun janyo naƙasu ga harkokin ilimi da kuma nazartar matakan da wakilan gwamnati ke ɗauka wanda ƙungiyar ta ce sam ba za su taimaka ba.