Bisa gayyatar shugaban kasar Zimbabawe Emmerson Mnangagwa, mataimakin shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Zhou Qiang, zai halarci bikin rantsar da shugaban, a matsayin manzon musammam na shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, bikin zai gudana ne yau Litinin a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp