A jiya ne, bisa gayyatar da shugaban kasar Mauritania Mohamed El Ghazouani ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Guangqian ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mauritania a birnin Nouakchott, babban birnin kasar. A yayin bikin, shugaba Ghazouani ya gana da Wang Guangqian, inda Wang ya isar da sakon murna da fatan alheri na shugaba Xi Jinping ga shugaba Ghazouani, ya ce Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tana son yin kokari tare da kasar Mauritaniya wajen kara amincewa da juna kan harkokin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa, da kara yin mu’amalar al’adu a tsakaninsu don bude sabon babi na raya dangantakarsu.
A nasa bangare, shugaba Ghazouani ya nuna godiya ga shugaba Xi Jinping bisa tura manzon musamman ya halarci bikin rantsar da shi. Ya bayyana cewa, kasarsa ta Mauritaniya ta maida hankali ga sada zumunci a tsakaninta da kasar Sin, tana son kara yin mu’amala da hadin gwiwa tare da kasar Sin a dukkan fannoni, ta yadda za a raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab Zhang)