ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

by Rabi'u Ali Indabawa
8 months ago
Tsaro

Shekaru da dama, sunan Kaduna ya zama abin tsoro ga matafiya da ’yan kasuwa. Al’ummomi masu rayuwa a yankunan Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da Kauru sun koma wuraren da garkuwa da mutane, kisan gilla da tashe tashen hankula suka mamaye.

Tsohuwar hanyar yaki da ‘yan ta’adda na hareharen soja, luguden bama-bamai daga sama da takaita lokacin fita, hakan ya kawo sauki na dan lokaci amma ba ta samar da zaman lafiya na dindindin ba. Maimakon haka, ya kara takurawa mutane ne kawai hakan ya kai ga samar da gibi tsakanin gwamnati da talakawa.

  • Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

Kididdiga sun nuna wani mummunan labari. Lokacin da amfani da hanyar ta karfi ya kai kololuwa, daruruwan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba sun mutu ko an raba su da muhallansu, dubban yara sun daina zuwa makaranta, kuma kasuwanni gaba daya sun durkushe. Kauyuka sun yi shiru saboda tsoro.

ADVERTISEMENT

Daga 2015 zuwa 2023, Kaduna ta fuskanci rikice-rikice 1,660, wanda ya janyo mutuwar mutum 4,876. A shekarar 2021 kadai, mutum 1,192 aka kashe, aka sace 3,348, sannan aka raunata 891. A kwata na farko na shekarar 2022, mutane 360 aka kashe, aka sace 1,399, a cikin watanni uku kacal.

A kananan hukumomi irin su Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da Chikun, adadin mutanen da suka rasa rayuka ya kai daga 400 zuwa 800 a kowane yanki cikin shekaru takwas. Wadannan ba lissafi ne kawai ba bala’o’i ne na dan’Adam da suka gwada karfin juriyar Kaduna da ruhinta.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’.

 

Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA

A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai.

A babban aikinsu na farko, ’yan bindiga sun saki fursunoni 58 ba tare da an harba ko da harsashi guda daya ba. Sakamakon matakan gina amana, an sake ’yantar da fiye da mutane 80 a cikin makonni kadan da suka biyo baya. Yau, adadin ya haura fursunoni 500, duk an sako su lafiya lau, babban tarihi a tsawon fafutukar zaman lafiya ta Jihar Kaduna.

“Zaman lafiya da muke ginawa a Kaduna ya ta’allaka ne a kan tattaunawa, ba mulki da karfi ba,” in ji Gwamna Uba Sani.

 

Mahimmin Sauyi: Tattaunawa da Bukatu

Nasara ta fara bayyana ne a zagaye na biyu na zaman tattaunawa tsakanin kwamitin musamman na ONSA–Kaduna da shugabannin Kungiyoyin makamai. Wannan ba irin tattaunawar da aka saba ba ce, amma an gina ta ne a kan gaskiya da fahimtar juna.

‘Yan bindiga sun gabatar da sharuddan su na zaman lafiya sun kuma hada da;

1. Sake bude kasuwannin yankunan.

2. Samun damar ‘ya’yansu na zuwa makarantu

3. Birnin Gwari, Giwa da Kudancin Kaduna su samu kulawa a asibitoci.

Maimakon a yi watsi da wadannan bukatu a matsayin dabara kawai, gwamnati ta gane cewa su ne ainihin bukatun ’yan kasa da ke tsakanin neman rayuwa ko mika wuya. Gwamna Sani ya gaggauta amincewa a bude kasuwanni, tare da umartar a dawo da al’amuran rayuwa yadda suka saba a yankunan da abin ya shafa.

An samu Sakamakon nan take kuma a bayyane. Hanyoyin da suka zama tamkar matattu a Giwa da Birnin Gwari yanzu sun cika da ayyuka. Matafiya sun tabbatar da cewa mutum na iya wucewa ta wadannan yankuna “ko da da daddare” kuma ya isa lafiya, abin da ba zai yiwu a tunanin mutane ba shekaru biyu da suka gabata.

 

Limaman addini, Turji da Muhallin Al’amura

A gefe guda, wasu malaman addini karkashin jagorancin Sheikh Musa Yusuf (Asadus Sunnah) sun bayyana a bainar jama’a cewa sun gudanar da tarurruka a cikin dajin da sanannen shugaban ’yan fashi Bello Turji da wasu kwamandojinsa.

A cewar rahoton jaridar Banguard ta ranar 5 ga Agusta, 2025, malamin ya bayyana cewa “an saki fursunoni 32 kuma an mika makamai” bayan tattaunawar da aka yi da Turji.

Wannan rahoton yana da mahimmanci ga tsarin sulhun Kaduna domin yana nuna yadda masu ruwa da tsaki na cikin gida da hukumomin yankin ke kirkirar damar shimfida zaman lafiya a matakin jiha: sakin fursunoni, ba da izini ga manoma su koma gonakinsu, da takaitaccen sauke makamai wanda ke rage cutarwa kai tsaye a kasa.

 

Daga ’Yan Fashi zuwa Masu wanzar da Zaman Lafiya

Watakila shaidar da ta fi daukar hankali game da wannan sauyi ita ce bayyanar tsoffin ’yan fashi da suka tuba, yanzu sun zama masu kiyaye zaman lafiya a yankuna da suka taba tarwatsawa.

A Birnin Gwari, tsohon fitaccen dan fashi ‘Jan Bros’ yanzu yana sintiri a cikin dazukan da shi da mutanensa suka buya a da, yana tabbatar da cewa babu sababbin barazana.

A Kudu maso Gabashin Kaduna, wani sanannen mutum da ake kira ‘Yellow 1 Million’ ya zama mai sulhu kuma mai fafutukar wanzar da zaman lafiya, sannan yana hani da tashin hankali.

Wadannan sauye-sauyen na iya zama kamar abin mamaki, kuma su ne sahihan ayyukan shirin zaman lafiya da ya yi kokarin tattaunawa maimakon kawar da su gaba daya. Kamar yadda wani masani kan tsaro ya ce, “Kaduna ta yi abin da wasu jihohi ke mafarkin yi, ta mayar da tsoffin abokan gaba zuwa masu rike da ragamar zaman lafiya.”

 

Samfurin Zamani lafiya

Samfurin Zaman Lafiyar Kaduna ba gwaji ne na lokaci daya ba, tsari ne mai dorewa, mai ci gaba da sauyawa.

A makon jiya ma, kwamitin musamman ya sake gudanar da taro, a wannan karon tare da shugabannin ’yan fashi, dagatai daga Kajuru, Kauru, Kagarko da Kachia, tare da sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi.

Taron, wanda Asadus Sunnah ya jagoranta, ya mayar da hankali kan karfafa abin da aka riga aka cimma da kuma hana komawar rikici.

Wannan ci gaba na tattaunawa, amincewa da sa ido, su ne suka bambanta hanyar Kaduna da wadancan yunkurin zaman lafiya na dan lokaci da aka yi a wasu sassan Nijeriya.

 

Farfado Da Tattalin Arziki: Zaman Lafiya Na Haifar Da Riba

Zaman lafiya ya fara haifar da sakamako a zahiri. Ayyukan noma a Giwa da Birnin Gwari da Kudancin Kaduna sun kai matakin da ya fi kowanne shekaru da suka gabata. Kasuwancin shanu, wanda matsalar tsoro ya dakile a da, ya sake farfadowa — yanzu manyan motoci 20 zuwa 30 na dauke da shanu suna bi ta hanyoyin da matsalar tsaro ya kange tsawon shekaru da dama.

Farfadowar kasuwanci ba wai ta tattalin arziki kadai ba ce; alama ce da ke nuna cewa an maido da mutunci da darajar al’umma.

“Duk wani kasuwa da aka sake bude nasara ce a kan tsoro,” in ji Gwamna Sani. “Duk wani yaro da ya koma makaranta shaida ce cewa tattaunawa na iya kayar da rashin bege.”

 

Samar Da Zaman Lafiya Ba Tare da Makami Ba A Yankunan Afrika

Sabon salon wannan aiki na Kaduna ya wuce iyakokin Nijeriya wajen tasiri. A fadin Afirka, al’ummomi sun dade suna gwagwarmaya da rashin nasarar amfani da karfin soja kadai. Daga shirin Afuwa na Yankin Neja Delta zuwa sulhun bayan kisan kare dangi a Rwanda, har zuwa tattaunawar da aka yi da rundunar Lord’s Resistance Army a Uganda — darasin daya ne: zaman lafiya na dindindin ba ya fitowa daga bakin bindiga ana gina shi ne ta hanyar shigar da kowa, tausayi da adalci.

Gwamna Uba Sani da tawagar ONSA sun daidaita wannan basira zuwa yanayin gida. Hanyar da suka bi ta nuna cewa ikon tattaunawa, idan an gina shi kan amincewa kuma doka ta tallafa, na iya dawo da zaman lafiya ko a wurare mafi tsauri.

 

Ka’idoji Uku Da Tushen Zaman Lafiyar Kaduna:

Ana samun zaman lafiya ne tare da tafiya da al’umma, ba wai a umarce su daga ofisoshin gwamnati ba. Sarakunan gargajiya, matasa, mata, da jami’an tsaro suna zama ne a tebur daya.

2. Shigar da Kowa cikin Tattalin Arziki: Farfado da kasuwanni, makarantu da asibitoci yana cire tushen da ke bai wa ’yan tawaye karfi.

3. Amincewa ta Hanya Mai Dorewa: Tattaunawa ta ci gaba, ba na lokaci-lokaci ba. Shigar ONSA yana tabbatar da rikon kwakwalwar hukuma da ci gaba a tsakanin hukumomi.

Wadannan ka’idojin sun yi daidai da abin da Babban Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkar, Nuhu Ribadu, ya lura, wanda a wata hira da Channels TB a ranar 29 ga Yuli, 2025, ya yaba da hadin gwiwar dabarar rashin amfani da karfi kuma ya tabbatar da cewa “daruruwan fursunoni sun sami ‘yanci a fadin kasa ta hanyar ayyukan zaman lafiya da aka tsara tare.” Ribadu ya kuma bayyana cewa “A yanzu samun sahihan bayanan sirri, shigar al’umma, da dakatar da harkokin ta’addanci na dindindin” maimakon kawai kai farmaki da kama mutane.

 

Mataki na gaba

Ko da yake har yanzu akwai wasu barazanar lokaci-lokaci, tubalan zaman lafiya a Kaduna sun fi karfi fiye da da. Gwamna Uba Sani ya tsaya tsayin daka: “Ba mu ayyana nasara ba; muna ayyana sadaukarwa. Kowace rana da muka kiyaye wannan zaman lafiya rana ce da ta kara kusantar da mu ga dorewar kwanciyar hankali ga al’ummarmu.”

Kalmominsa yanzu suna yaduwa a cikin Birnin Gwari da sauran sassan Kudancin Kaduna da Giwa wadanda a da ake jin harbin bindiga, amma yanzu aka maye gurbinsu da dariyar yara da kuma walwalar kasuwanci.

 

Darasi Ga Nijeriya Da Afirca

Dabarun wanzar da Zaman Lafiyar Kaduna shi ne shaida wa mai rai cewa ko a cikin mafi hadarin yankin Nijeriya, zaman lafiya na iya samu ta hanyar tattaunawa kuma da hanyar ci gaban al’umma. Yana tabbatar da gaskiya mai sauki ba tare da tsorata dan’Adam ba.

Ta hanyar hadin gwiwa da Ofishin Mashawarcin Tsaron Kasa, Gwamna Uba Sani ya nuna cewa yakin neman zaman lafiya ba a kan dazuka ko hare-haren sama ake samun nasara ba, sai ta dabaru cikin zukatan da suke shirye su yafe, shugabanni kuma su shirya su saurari al’ummar da suke da karfin gwiwar sake ginuwa.

Tsaro
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.