Muna kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bara, lissafin zai ba ka cewa a baran Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A bana kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.
Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal mai zuwa lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. ɗomin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron ƙasa yanzu ya ƙara wasu shekaru 500 a raye.
- Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
- Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).
Abin da Ya Sa Ba A Haɗe Farkon ƙirgen Shekarar Hijira da Ranar Yaƙin Badar Ba
Alhamdu lillah, mun ji dai karatu a kan ranar haihuwar Manzon Allah (SAW) da ranar Manzanci da irin muhimmancinsu, amma duk da haka Sahabbai (RA) ba su daidaita tarihin shekara da su ba, sai tarihin Hijra saboda sanin muhimmancin yin hakan.
A yau kuma za mu mayar da hankali ne a kan rana babba, ita ce ranar Yaƙin badar. Allah yana ce mata ‘ranar rarrabewa’, ranar da aka rabe ƙarya da gaskiya, ranar da Jama’ar Allah suka zama daban, na Shaidan ma suka zama daban, ranar da rundunonin mutane guda biyu suka haɗu, rundunar Allah da rundunar Shaidan. Rundunar Allah shugabansu Annabi Muhammadu (SAW). Rundunar Shaidan shugabansu Abu Jahli.
A wannan rana ce Allah ya halatta kare kai, duk yaƙoƙin da Manzon Allah (SAW) ya yi kamar yadda Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya fada, ba ya yisu ne don ya tilasta wa kafirai su karɓi Musulunci ba. Manzon Allah (SAW) ya fi so mutum ya karɓi Musulunci da kyakkyawar zuciya, da ƴancinsa, da jin cewa yana son Musuluncin a ransa. Kowa yana da hankali, don haka kowa ya ga abu mai kyau ya sani, haka in ya ga abu mara kyau in dai ba kuma shaidan ya shiga cikin lamarin ba. Idan ma mutum kokwanto yake a kan abu, ka iya ba shi shawara da kalamai masu daɗi, ba zancen fada, ba zancen yaƙi. Allah Ta’ala ya ce “ba dole a cikin addinin nan”.
Ranar Badar rana ce ta rarrabewa, dama kafirai sun yi ta cutar da Manzon Allah (SAW) ba ya ramawa. Ranar Badar Mala’iku ma sun yi yaƙi domin nuna gaskiyar Musulunci ƙuru-ƙuru a gani. ɗuk wani yaƙi na rabe gaskiya da ƙarya har duniya ta naɗe zai zamo daga albarkar Yaƙin Badar ne, domin da ba a ci nasarar Yaƙin Badar ba da komai ya ƙare, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya nunar lokacin da ya ce, “Allah in har ka bari aka halaka wadannan mutanen (Sahabbai) ba za a ƙara bauta maka a kan ƙasa ba”. Kuma Manzon Allah (SAW) ya nuna wa duniya irin alherin da ke cikin Musulunci, illa kawai dai wanda ya so ya yi imani, wanda ya ƙi kuma shi ya so.
Yaƙin Badar ba yaƙi ne na neman mamaya ba, Manzon Allah (SAW) ya toshe shisshigi ne da ƴantar da Bayin Allah da ake bautar da su da zalunci. Ya nuna wa duniya hukunce-hukuncen yaƙi mafi dacewa da tausayin dan Adam da kyautata masa. A ranar Badar Yahudawa sun yi imani tare da tabbatar da cewa lallai wannan Annabi shi ne Annabin ƙarshe kamar yadda suka karanta a Attaura, duk kuwa da cewa tun kafin yaƙin sun ga alamomin hakan. Amma su cewa suke mutum ba zai zama na Allah ba sai in yana samun nasara a kan abokan gaba, wannan kuma daga garesu ne kawai. Saboda misali, duk idan wani ya ce mutum ba zai zama na Allah ba sai ya zama mai kuɗi, ko sai ya zama talaka, ko sai ya zama malami, ko sai ya zama jahili to bashi da ma’aunin gane haka. Shi Allah Tabaraka wa Ta’ala ta shi ake gane shi, amma ba ta wani abu ba. ɗuk wani abu da za ka gani kyauta ce kawai ta Allah. To, Yahudawa sun yi imani da Annabi (SAW) a ranar Badar, sai dai daga baya suka warware.
Yusufun Nabahani (RA) ya fada a cikin Littafinsa na Anwarul Muhammadiyya cewa tun da aka yi Yaƙin Badar Allah ya ajiye wasu Mala’iku da dunfufofi suna ta bugawa domin murnar nasarar Badar kuma ba za su bari ba har tashin duniya, duk wanda Allah ya yi masa gamo da katari idan ya je Badar zai ji.
Allah kuma mai iko ne ya shigar da wani Bawansa cikin ƴan Badar duk kuwa da cewa bai yi yaƙin ba. Idan mutum ya yi wani ƙoƙari Allah ya duba sai ya yi masa hakan, bare kuma Khalifan Manzon Allah (SAW) ya ce ma Allah zai tasheka a cikin ƴan Badar. ɗomin da yawa akwai wadanda ba a yi Yaƙin Badar da su ba sun tambayi Manzon Allah (SAW) cewa a raba Ganimar Badar da su, Manzon Allah ya amince, wani ma ya tambayi ladan fa, Manzon Allah ya ce har da ladan. To yanzu dai ganima ta ƙare, amma mutum zai iya yin wani ƙoƙari Allah ya duba ya sa shi a cikin ƴan Badar ba dole sai yaƙi ba. Misali, idan mutum ya yi wata ƙasaitacciyar gona ya ciyar da al’ummar Annabi (SAW) Allah zai iya sa shi a ciki, haka in ka yada zaman lafiya a cikin al’ummar Annabi ko yada sanin Allah, duk dai Allah mai iko ne ya shigar da mutum cikinsu.
Sahabban da suka yi Yaƙin Badar suna da wata falala ta musamman ta yadda idan aka yi wani taro ana ba da labarin wadanda suka halarta akan ce Sahabban Manzon Allah sun je wurin har da ƴan Badar. Haka nan ko Hadisi ne wani ya ruwaito a cikinsu za ka ji bayan an ambaci kasancewarsa Sahabin Annabi akan ƙara da faɗin falalarsa cewa dan Badar ne. daraja ce babba, ƴan Badar Alheri ne.
Kuma har ila yau, yana daga falalar Badar a ranar Sahabbai Muhajirai da Ansaru suka haɗu a abu guda daya, wato ana kiransu da sunan ƴan Badar dukansu. daga ƴan Badar sai ƴan Ukhudu, sai ƴan Bai’atur Ridwani, sannan ƴan Fatahu Makkata kuma dukkansu masu girma ne a wurin Allah.
Masu karatu kun ga dai duk da abubuwan da Ranar Badar ta tara, Sahabbai ba su fara ƙirgen shekara da ita ba sai a ta Hijirah domin hikima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp