Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadin aiki a lardin Sichuan dake yammacin kasar Sin, inda ya ziyarci wani kamfani mai zaman kansa mai suna Gimi, dake kera kayan laturoni, da na samar da wutar lantarki.
Shugaba Xi ya shiga dakin nune-nune da sashin kere-kere na kamfanin, inda ya kara fahimtar yadda kamfanin ke gudanar da ayyukan kirkire-kirkire da nuna goyon-baya ga raya tattalin arzikin wurin da sauransu, al’amarin da ya sake shaida cewa, kasar Sin na matukar maida hankali, gami da nuna goyon-baya ga raya tattalin arziki mai zaman kansa.
Sakamakon yaduwar annobar COVID-19, da sauye-sauyen halin da ake ciki na gida da waje, da rashin sanin tabbas, kamfanoni masu zaman kansu na kara fuskantar kalubaloli, inda gwamnatoci a matakai daban-daban na kasar Sin ke lalibo hanyoyi daban-daban da tallafa musu don haye wahalhalu da samar da ci gaba.
A yayin ziyarar shugaba Xi a wannan karo, ya ganewa idanunsa manufofin gwamnatin wurin na taimakawa kamfanonin dake fuskantar matsala.
To shin ko ina mafita ga kamfanoni masu zaman kansu, don samun sabbin damammaki a yayin da suke fuskantar matsaloli da sauye-sauye? Amsar nan ita ce, yin kirkire-kirkire.
Kamfanin Gimi da shugaba Xi ya ziyarta a wannan karo, kamfani ne dake kan gaba a kasar Sin a bangaren samar da na’urorin kera allon majigi, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, ya dace a inganta karfin yin kirkire-kirkire, da gaggauta raya kasar Sin har ta zama kasa mai karfin kere-kere.
Kalaman Xi sun karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin, don shawo kan kalubaloli da samar da ci gaba, kana, za su kara taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)