A karo na biyar a cikin watanni biyu, shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya samu karin lambar yabo.
Idan ba a manta ba dai a watan da ta gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Marwa sau biyu, inda ya ba shi lambar yabo ta kasa matakin CON, kazalika, kuma ya kara karrama shi bayan mako guda da lambar yabo bisa bajintar da ya nuna a yaki da miyagun kwayoyi.
Biyo bayan wadannan karramawar ne, kungiyar al’umman garin Michika na Jihar Adamawa suka yi taro na musamman, inda suka karrama Marwa a matsayin dansu da ya nuna bajinta na musamman a Nijeriya. Kungiyar ta karrama shi ne tare da wasu fitattun ‘yan garin na Michika.
Babu shakka bajintar Marwa na inganta yaki da ta’amuli da miyagun kwayoyi abu ne da ya bayyana, lura da nasarori da hukumar NDLEA take samu a kullum. Ko a yau, hukumar ta fitar da sanarwar kama sama da tan bakwai na wiwi wanda yawan sa ya haura kilogiram dubu bakawai.
Alkaluman bayanai sun yi nuni da cewa, hukumar NDLEA ta kama sama da mutane 8,996 a cikin shekarar 2022. A bangaren kayan maye kuma, hukumar ta kama sama da kilogiram 219,576 na miyagun kwayoyi a wurare daban-daban a Nijeriya a cikin shekarar nan. Kazalika, hukumar ta lalata gonakin wiwi wanda yawan su ya kai hekta 324. Haka ma hukumar ta yi nasarar gyara tunanin (rehabilitation) na mashaya 6,244 a cikin shekarar nan.
A kwanan nan ne hukumar ta yi shahararren kamun nan da ta yi na hodar iblis wanda yawansa ya kai tan 1.8 a wani gidan ajiya a Jihar Legas. Hodar iblis din wanda aka kiyasta kudinsa ya kai Naira biliyan 194, ya kasance kamu mafi girma na hodar iblis da hukumar ta yi a lokaci daya tun bayan kafa hukumar a shekaru 30 da suka wuce.
Adadin nasarorin da Marwa ya samu a yayin shugabancin hukumar NDLEA ba za su kirgu ba. Kuma wannan ba shi ne karshe ba, saboda har yanzu bakin alkalami a jike yake da tawadar rubuta nasarori da hukumar take ci gaba da samu a yaki da fataucin miyagun kwayoyi.
Idan akwai abun da Marwa ya nuna wa duniya da ya kamata na baya su yi koyi da shi, to ba zai wuce tsayuwa da gaske wajen aiwatar da aiki a duk inda ya samu kansa ba. Za a gane hakan idan aka waiwaya zuwa mukaman da ya rike a baya, kamar na gwamnan Jihar Legas da makamantansu.