A jiya ne, masana kimiyya daga kasar Sin da Afirka suka sake jaddada kiran da ake yi na inganta tsare-tsaren noma da suka dace da yanayi da kuma jure matsalar sauyin yanayi, domin shawo kan matsalar yunwa da ta abinci mai gina jiki.
A jawaban da suka gabatar yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, masanan sun amince da matsalar yunwa dake karuwa a Afirka, inda suka jaddada cewa, mafita mai dorewa ita ce koma wa ga ingantattun hanyoyin samar da abinci dake iya jure matsalar sauyin yanayi.
Darektan shirin hadin gwiwa na kasa da kasa a kwalejin kimiyya ta kasar Sin Yan Zhuang, ya ce yaki da matsalar sauyin yanayi da sauran matsaloli da suka shafi muhalli a nahiyar Afirka, zai dora nahiyar a kan hanyar samar da abinci na dogon lokaci. Yana mai cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, zai taimaka wajen inganta matakan yaki da matsalar sauyin yanayi a Afirka da kuma gaggauta cimma burin ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030 kan kawar da yunwa a nahiyar.
Kimanin masanan kasashen Sin da Afirka 100 ne ke halartar taro karo na uku kan sauyin yanayi da muhalli da zaman rayuwa da ke gudana a birnin Nairobi, don tattauna sabbin hanyoyin inganta abinci da abinci mai gina jiki a Afirka. (Ibrahim Yaya)