Masana a cibiyar bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari a Nijeriya sun nuna damuwarsu a kan yadda ake kara samun takurawa ta hanyar sabbin ka’idoji da dokoki daga hukumomi masu sa ido a harkokin kamfanomi masu shigowa domin zuba jari a tattalin arzikin kasa.
Daraktar Cibiyar, Dakta Muda Yusuf ya bayyana cewa, sau dama ana samun wuce goda da iri daga hukumomi masu sanya ido inda sukan sa haraji da tilastawa masu zuba jari sai sun biya tare da kuma yi musu barazana wanda haka yana kawo cikas ga masu yukurin shigowa domin su zuba jari a Nijeriya.
- Jihohi Sun Kashe Naira Biliyan 139.92 Wajen Biyan Bashin Kasashen Ketare A Wata 6
- Ya Kamata Tuba Daga Laifin Yaki Da Tsoffin Sojojin Japan Ke Yi Ya Zama Matsaya Guda Ta Daukacin ‘Yan Siyasar Japan
Ya kuma lura da cewa, akwai kuma damuwa a kan yadda ake samu hukumomi fiye da daya suna kokarin karbar haraji iri daya daga masu zuba jari, ko kuma a samu wasu na shiga cikin aikin wasu wanda hakan yana takura masu sabbin kamfanoni da suka shigo domin zuba jari a kasar nan.
A kan haka ne suka nemi hukumomin su yi taka tsantsan wajen gudanar da aikin su ta yadda masu zuba jarin ba za su fice ba, su yi amfani da karfinsu wajen karfafa kudurin wannan gwamnati na Bola Tinubu wajen karfafa harkokin kasuwanci da kasashen waje ta yadda kasar za ta samu kudaden shiga da za ta gudanar da ayyukan raya kasa.
Ya kuma ce, kamfanoni na fuskantar matsaloli da dama a kasar nan kuma bai kamata a kara musu wasu matsalolin ba, matsalolin da suke fuskanta sun hada da na rashin isasshen wutar lantarki, tsada da karancin man fetur, rashin tsaro da kuma rashin tabbas ga darajar naira. A kan haka ya kamata ne mu rungumi abubwuan da za su karfafa masu zuba jari ba wai a takura musu ba.
Ya kuma nemi dukkan masu zuba jari a kasar nan su tabbatar da suna mutunta dukkan ka’idoji da dokokin kasa wajen gudanar da harkokinsu.