A kwanan nan ne sashen watsa shirye-shirye a yankunan Asiya da Afirka na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), tare da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke wasu kasashe, da cibiyoyin nazari na wurin, suka shirya wasu tarukan kara wa juna sani a kasashen Pakistan, Philippines, Cambodia, Laos, Kenya, da Turkiya, game da shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) da kasar Sin ta gabatar.
Jami’ai, masana da wakilan kafafen yada labarai sun ce, shawarar ta gabatar da yadda za a cike “gibin jagoranci” na duniya tare da samar da ingantaccen tsari don magance babakeren bangare guda, da karfafa fada-a-jin kasashe masu tasowa da samar da tsarin kasa da kasa mafi adalci.
Shahararren masani kan harkokin kasa da kasa na kasar Kenya Cavince Adhere, ya yi imanin cewa, wasu hukumomi da cibiyoyi na kasa da kasa sun dade a karkashin ikon wasu kasashe, kuma galibi ana yin watsi da muryoyin kasashe masu tasowa. A yayin da ake fama da “gibin jagorancin” duniya, al’ummomin kasa da kasa na bukatar mafita ta gaskiya da adalci cikin gaggawa. Gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya “ta dace da buri na bai daya na duk jama’ar kasashe kuma tana kunshe da biyan bukatun harkokin duniyar yau cikin gaggawa.”
Shi ma da yake bayani a wajen taron, Patrick Maluki, shugaban tsangayar nazarin harkokin waje ta jami’ar Nairobi ta Kenya, ya bayyana cewa, shawarar da Xi Jinping ya gabatar ta samar da wani sabon dandali ga kasashen Afirka na shiga harkokin kasa da kasa da samun ci gaba mai dorewa. Ya ce, “A tarihi, an dade ana mayar da Afirka saniyar ware. Muhimman ra’ayoyin da ke cikin shawarar sun yi daidai da bukatun ci gaban Afirka. Ya kamata kasashen Afirka na yau su zama masu shiga a dama da su sosai a harkokin jagorancin duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp