A ranar Litinin 17 ga Fabrairu, 2025, na sami damar tsayawa tare da manyan mutane a wani taron kaddamar da bikin bayar da lambar yabo ta ‘Family Special Award Night’, wanda Hindatu Bashir ta shirya, Ga wadanda suke sabbi a kan tarihin masana’antar Kannywood su sani cewa, Hindatu Bashir ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman fina-finan Hausa a shekarun 1990.
Taron wanda ya kunshi dadaddun jarumai masu kima a masana’antar Kannywood wadanda suka yanke wa masana’antar cibiya a shekarun 1990 zuwa 2000, ya sake nuna yadda mazan jiya suka yi tsayin daka wajen ganin abin da ake kira Kannywood ya zama abin da ya zama yanzu,”Mu hadu a Bata” wata kalma ce da duk wanda yake cikin masana’antar shirya fina-finai a wadancan shekarun ya sani, wadda ke nuna yadda ake haduwa a rukunin shagunan Bata da ke fuskantar kasuwar Sabon Gari a Kano domin gabatar da al’amura da su ka shafi hotuna masu motsi, wannan zai nuna maka irin gwagwarmayar da wadanda ke wannan taro su ka yi kafin yanzu.
- Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
- Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa
Wadannan tsofaffin jarumai sune su ka haifar da masana’antar da muke gani a yanzu a matsayin Kannywood, daya daga cikinsu Sunusi Shehu, shi ne wanda ya kirkiro kalmar “Kanywood” kafin ta zama “Kannywood”, wannan kalma ta Kannywood ta shiga cikin kamus na Turanci na Odford a cikin shekarar 2019 wanda ya bayyana Kannywood a matsayin “masana’antar shirya fina-finai ta Kano wadda ke fitar da manyan mashahuran wakokin soyayya na harshen Hausa a kowace shekara”.
Yayin da wadannan dattawan suka samar da wannan masana’antar, wadanda su ka zo daga baya ne su ka sami dimbin alheri a cikinta su ka ci gaba da yin fina-finai da ke kwailwayon fina-finan kasar Indiya.Wadannan dattawa sun ja baya ba don basu iyawa ba sai dai domin bahaushe ya ce “Ba ka lokacinka ka yi na wani” aka barsu da tunanin rawar da su ka taka ta domin kankanen lokaci da kuma rashin kwarewa da samun tallafi da su ka yi fama dashi a wancan lokacin, sannan da rashin amfani da damarsu a lokacin da su ka sameta a babbar masana’antar ta fina-finan Hausa.
Misali, yayin da wasu kadan daga cikinsu ke da alaka da wasu kamfanonin talabijin a wancan lokacin kamar marigayiya Amina Garba Dumba (kamfanin sadarwa na Starcomms), rashin tuntubar jami’an wadannan kamfanoni domin tallata fuskarsu a wancan lokacin na daga cikin damarmakin da su ka subuce masu, damar da sababbin masu shigowa suka yi gaggawar amfani da ita, amfani da zamanantar da Duniya ta yi na tallace-tallace na daga cikin abinda ya taimaki kyawawan mata da samari a wannan karni a masana’antar Kannywood yanzu.
Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo.
Dukkanmu sai muka tuna da fim dinsu na Badakala (wanda wani jarumi Bashir Mudi Yakasai ya shirya), inda suka yi fim mai dauke da rawa da waka na farko a cikin fina-finan Hausa,wato a shekarar 1997 wannan fim ya daga abinda yanzu ake kira Hausa Afropop, domin shi ne wakar fina-finan Hausa ta farko da aka kai wa Rabi’u BK a kasuwar Kofar Wambai domin sayar da shi a matsayin shirin waka mai zaman kansa, Dan Azumi Baba, wanda ya rubuta labarin, ya na nan tare da su a wannan babban taron.
Tsoffin jaruman Kannywood a bisa wata kungiya mai zaman kanta wadda akasari mata suka kafa wacce a yanzu na ke kira “Hausa Classic Cinema” karkashin jagorancin mutane irin su Wasila Isma’il, sun yanke shawarar gudanar da taron shekara-shekara domin yaba wa kansu da kuma wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban masana’antar.
Ni dai ban san su ba, kuma Hindatu Bashir da ta shirya taron na shekarar 2025 sai da ta bi ta hannun mutane biyu domin su zo wurina su kawo mani goron gayyata, Hamisu Lamido Iyan-Tama ya kira ni ‘yan sa’o’i kadan kafin taron ya nemi in halarta, mutane biyu ne kacal a Kannywood da za su umarce ni da in yi irin wannan abu, kuma zan yi su ne Hamisu Iyan Tama da Alkanawy, da na shirya sai na tafi tare da dana Munzir.
Wadannan tsofaffin jarumai sun kasance fuskokin fina-finan Hausa na gargajiya da labarun soyayya, eh labarun soyayya da a kan iya samun rikice-rikice na cikin gida sanadiyar soyayya kuma a samu mafita cikin sauki ta hanyar salo daban-daban, ba tare da sun nuna wani abu na tsiraici ba saboda dukkansu sun mallaki hankalinsu tun kafin su shiga harkar, saboda haka dole ne su tsare mutuncin kansu da na iyalinsu.
Manyan dattawan jarumai da su ka halarci wannan taron a ranar akwai Ado Ahmad Gidan Dabino, Dan Azumi Baba, Balaraba Ramat Yakubu, Bala Anas Babinlata, Hamisu Lamido Iyan-Tama da sauran wadanda su ka kafa kuma su ka zage damtse wajen ganin masana’antar ta tsayu da kafafunta tun daga shekarun 1990 zuwa yanzu, dayan jinsin kuma akwai dattawan jarumai mata kamar ita kanta da ta shirya taron Hindatu Bashir, Hajara Usman, Hadiza Kabara, Ladin Cima, Maijidda Abbas, Rukayya Dawayya, da wasu da yawa da ba zan iya tunawa ba.
A bangaren mu da muke zaune a teburin manyan baki kuwa akwai Muhammadu Rabi’u Rikadawa, sai Dan Azumi Baba, ni kaina, Ado Ahmad, Hajiya Balaraba, Ladi Cima da Hajara Usman,na yi matukar farin ciki da kasancewa cikin wadannan yan wasan kwaikwayo da furodusoshi,dukkan wurin cike yake da mutane, har ba za mu iya ganin sauran wadanda ke zaune a wannan teburi na manyan baki ba, amma dai na san cewar su ma sun bayar da irin tasu gudunmawar wajen wannan babban aiki da aka faro shekaru fiye da Talatin da su ka wuce.
An bai wa Ado Ahmad Gidan Dabino lambar yabo ta “Trailblazer Award, a matsayin wanda ya share fage ga al’ummar da su ka shigo Kannywood ta hanyar wani shiri nasa mai suna “In Da So Da Kauna”, fim din ya fayyace irin nau’in soyayya tun daga farko,ya kuma hada da hakikanin tarihin rayuwar Hausawa tare da hasashen goben bahaushe wanda a wancan lokacin har littafi ya rubuta akan wannan makala.
An bai wa Dan Azumi lambar yabo ta “Star Producer Award” bisa la’akari da rawar da ya taka a masana’antar nishadin Hausa baki daya, tabbas hakane, domin shi ne ya gano Hamisu Lamido-Iyan-Tama, babban dan wasan kwaikwayo mai ban sha’awa wanda zai iya tsayuwa a duk inda wani jarumi ya tsaya ko da kuwa a masana’antar Hollywood ne.
Abin ban mamaki duka biyun Dan Azumi da Ado sun fara zama kwararrun marubutan Hausa kafin su yi kaura zuwa masana’antar fim a matsayin uwayen da su ka kafa ta, a tsakiyar shekarun 1990, a farkon shekarar 2000 an mayar da su zuwa matsayin mashawarta kawai, rawar da su ka taka a cikin manyan fina-finai na baya bayan inda Ado Ahmad ya fito a matsayin Gwamna (Kwana Casa’in) wanda shirin siyasa ne, da Dan Azumi a matsayin Kamaye a shirin Dadin Kowa, wanda akayi saboda hadin kan al’umma, ya nuna cewar DA TSOHUWAR ZUMA AKE MAGANI, don kuwa bani tunanin akwai wani daga cikin matasan jarumai na yanzu da zai yarda ya taka irin wannan rawar.
Balaraba Ramat Yakubu ta samu lambar yabo ta “Legendary Producer Award, inda aka karramata da lambar yabo ta furodusar da ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban masana’antar Kannywood, fina finanta irinsu Sai A Lahira” da “Alhaki Kwikwiyo” za su dade ana tunawa dasu a tarihin wannan masana’antar a kodayaushe, abinda na kira “Kannywood Classics”, Hamisu Lamido Iyan-Tama ya sami shaidar wani mutum da ya nunawa manyan gobe hanyar da ya kamata su bi a wannan masana’antar.
An ba ni lambar yabo ta “Special Recognition” a matsayin wadanda ba jaruman fim ba amma kuma su ka bayar da gudunmawarsu ta wata sigar, amma kuma sun cancanci karramawa saboda irin gudunmawar da suka bayar ta hanyar inganta da kuma kiyaye al’adun Hausa ta hanyar fim”, duk da cewar rukunin gajerun bidiyo ya kamata ace na fito amma dai wannan kyautar na dauke ta a matsayin karramawa ta musamman a wajena.
A kan dandamalin “Red Carpet”, an tambaye ni yadda na ji game da taron, sai na mayar da martani cewa taron ya fayyace ainahin abinda ake kira Da Tsohuwar Zuma Ake Magani, duba da dimbin taurarin da su ka halarci taron, wadanda su ne uwa da magoyiyar masana’antar nishadin zamani ta Hausa, wadannan taurari sun samar da fina-finai masu tsafta, wanda ake yaba wa kuma ana kiransu da ‘Classics’.
Sun gabatar da fina finai na Iyali da sauran abubuwan da su ka shafi rayuwar Malam Bahaushe, amma da wasu su ka zo sai suka yi watsi da wadannan fina finai suka kama wasu labaran karya game da Hausa da rayuwarsu, irin wadannan tsofaffin gwanaye wadanda ke da tsantsar sani na al’adar fina-finan Hausa ne za su kai ga farfado da fina-finan Hausa, su ne za su jagoranci hanyar kai masana’antar Kannywood zuwa Tudun Mun Tsira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp