• English
  • Business News
Sunday, August 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
7 hours ago
in Nishadi
0
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun Jarumai, manyan da kanana, har ma da mawaka, daga cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar, da ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar Kannywood, wato HAUWA GARBA wacce aka fi sani da SABURA Gidan Badamasi. Inda ta bayyanawa masu karatu wasu matsaloli da ke cikin masana’antar Kannywood, tare da irin kalubalen da suke fuskanta wajen masu kallo, har ma da wasu bayanan masu yawa da suka shafi sana’arta ta fim.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki, tare da sunan da aka fi saninki da shi.

Sunana Hauwa Garba, wacce aka fi sani da ‘Yar’Auta ko Sabura ta gidan Badamasi.

 

Labarai Masu Nasaba

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

An haife ni a garin Kano a Bichi LGA, na yi firamare a Bichi ‘Chiranci Primary School’. Amma ban cigaba ba da yake mu fulani ne, daga nan aka yi min aure. Bayan na fita daga gidan mijina, sai na fara koyan wasan dabe (Drama), daga nan ne dai na samu kaina a cikin wannan sana’ar.

 

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?

Abin da ya ja hankalina har na fara fim, bayan na yi aure na auri dan fim, Allah ya ji kanshi Rabilu Musa (Ibro). Bayan na fita daga hannunsa kawai sai na yi sha’awar ni ma na fara fim. To, akwai wacce nake so a ‘yan fim Fati Muhd, lokacin ni masoyiyarta ce, ina son aktin dinta. Daga nan ne na tsunduma na samu Baba Ari, da Musa Maisana’a, da Dan’Auta, da marigayi Cinnaka, sune suka jajirce akan na je na yi fim. Saboda muna zuwa wasan dabe, suka ce ya dace na shiga fim kowa ma ya san da ni.

 

Bayan fitowa matsayin jaruma, ko akwai wani bangare da ki ke taka rawa a cikin masana’antar?

Gaskiya ni jaruma ce kawai, ba na daukar nauyi ko shiryawa ko makamantan haka, ni dai kawai jaruma ce.

 

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

Lokacin da na fara fim, gaskiya ban samu wani matsaloli ba. Saboda ni ba a budurwa ta na fara fim ba, daman wacce take fara fim a budurwar ta, ita ce ke samun matsala. Ni na fara fim bayan na fita daga gidan mijina, kuma wanda na aura dan fim ne, saboda haka dan na shiga fim ba zan samu wani gwagwarmaya ba. Inda zan samu, da a wajensa zan samu a rika cewa ai dan fim za ta aura. Amma kowa jin dadi yake ma zan auri dan fim, wajen ‘yan’uwa da dangi dukka ban samu matsala ba. Kuma ban je wajen wani furodusa ko darakta ba, imu-imu su Dan’auta da Baba Ari muka hada muka yi finafinan mu. Akwai Aminu Dagash, akwai darakta K-Eza su ne suka yi min finafinai biyu, mu ma muka hada group din mu, muka yi finafinai biyu. Dan haka ban sha wata wahala ba.

 

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Gaskiya ba zan iya tantance adadin finafinan da na fito ciki ba, na dai yi finafinai da yawa, amma ba zan iya tantance guda nawa nayi ba.

 

Wacce rawa ki ka fi yawan takawa a masana’antar Kannywood?

Rawar da na fi yawan takawa ita ce; rawar ‘Yar’Auta, shagwababba, kuma kamar irin doluwa, gabuwa, irin bazar-bazar din nan, duk dai irin haka.To, ko uwa na fito bana yin kyau, sai dai in uwar ita ma bazar-niya ce. Amma indai ba haka ba, ba na yin kyau. Ana iya saka ni a ‘yar aikin gida, ko ‘yar gida, amma ga ni ga yadda nake shawaragi-shawaragi.

 

Ya ki ka tsinci kanki a cikin shirin Gidan Badamasi?

Na tsinci kaina a jaruma, tunda jarumar ce daman, shi ya sa na tsinci kaina a jaruma. Saboda ni abin da nake gani a rayuwa, duk abin da ka ga ka yi sana’arka ce kuma aikinka ne.

 

Wane waje ne ya fi baki wahala a cikin shirin gidan badamasi?

Wajen da ya ban wahala kwarai akwai, wajen kuwa shi ne, inda nake zuwa nake marin Azima ta yi shigar buzaye ta saka nikab. Duk ‘yan gidan na tsoro, ni kuma ban san wace ce ba na dauka irin buzayen nan ne, ta ki kuma magana kuma gashi da daddare. Na yi ta magana taki magana ni kuma na kwada mata mari, tana bude fuska har zuciyata na ji ba dadi. Dan kafin ma a yi abun, an gwada an gwada na ki, sai da Baba Falalu ya ce “Ke ba fa gaskiya bane, ki daure ki abun nan ‘normal”, sannan na yi.

 

Bayan Jaruma Fati Muhd da ki ka ce tana burge ki kafin ki fara fim, ko akwai wasu Jaruman da suke burge ki a wancen lokacin?

Bayan Fati Muhammad da take burge ni a mata, dan saboda ita ne ma na kirkiro wannan ‘makeup’ din da nake yi wa kaina. Sai kuma a maza S.Nuhu, muna son shi, dan ba ni kadai ba ma muna son shi. Allah ya ji kansa ya gafarta musu, irin su; Hauwa Ali Dodo, akwai wata babbar jarumata ita tana nan Hindatu Bashir, Allah ya kara mata lafiya.

 

Me ya ja hankalinki har ki ka kirkiri kwalliyar fuska saboda Fati Muhammad?

Ni masoyiyar Fati Muhammad ce, kuma ta taba zuwa Abuja ana wasa, mu kuma lokacin mun je biki a lokacin aka ce mana Fati Muhd za ta yi wasa. Duk ‘yan matan unguwarmu da muka je bikin da su muka ce mu je mu gani. Muka hada kudi muka bayar da kudin ‘gate’ muka shiga muka zauna, har muna dan tsoro daga can sai ga ta, ta shigo ita da Lawan Ahmad. Wajen ya cika sosai, tana shigowa muka ce indai aka tashi sai mun yi mata magana, ana gamawa muka fita waje muna jiranta. Wajen ya cika makil ta fito ana kakkarewa ta shiga mota, duk da cewa akwai ‘yan sanda a wajen, amma mutane sai kai hannu ake ana shafa motar. Motar da ta shiga kowa yake tabawa yana shafawa a jikinsa ana ta Fati Muhd, ni kaina sai da na kai hannu na shafo motar na shafa a jikina. Tun daga wannan lokacin na ce, in Allah ya yi maka daukaka in ba kada masu bin bayanka za ka samu matsala. Daga nan sai na ga a gwababba zan fito, tana iya yuwa ka yi kwalliya irin ta yara ka damalmale fuska, kawai sai na dauko wannan kwalliyar na damalmale fuska. Sai ga shi ina yin aiki da ita, Allah ya sa ‘yan kallo da masu kaunar aikinmu suka kaunata.

 

Ko akwai wani fim da ki ka taba fitowa ba tare da kwalliyar fuskar da ki ke yi ba?

Gaskiya ban taba fitowa fim din da ba wannan kwalliyar ba. Saboda ni kaina bana so na fito a fim din da ba wannan kwalliyar. Ba wai bana so bane, ina so amma in na fito ba zan yi kyau ba, tunanin da nake yi kenan. Ba zan yi kyau ba, kuma ba zan bayar da abin da ake so ba, idan na yi kwalliyar tana kara zaburar da ni ga abin da zan yi. Amma dai zan gwada watarana na yi fim ba wannan kwalliyar, na gani ko zai yu.

 

Ya za ki bambantawa masu karatu, bambancin finafinan baya da na yanzu?

Bambancin shi ne; yanzu an samu cigaba sosai, wajen kyamera, wajen samu, ‘location’ din ma gaskiya an samu abubuwa masu kyau. Kawai abin da dai muka rasa saka kaya, kayan ‘da’ a rufe suke duk jikinka kuma sun yi maka yawa, ba lallai ne a ga surarka ba. Na yanzu kuma a matse suke, shi ne kawai matsalar mu a yanzu. Allah ubangiji ya shirya ya gyara mana.

 

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

To, Alhamdulillahi na samu nasarori kala-kala, tunda a cikin fim din nan, ‘da’ ba ni da gida kuma na dawo ina da gida ko na ce gidaje ma, har na dawo ban taba tunanin zan hau mota ba, na hau mota tawa ta kaina. Sannan kuma duk irin masu kudi haka ko ‘yan siyasa, ‘yan majalisa matansu za su ce a kai mu. Ana kai mu wasu ma za a ga kyauta ne kawai za ka samu, wacce za ka gigice. Saboda jin dadi wannan ma nasara ce. Sannan nasara ta biyu duk inda ka je an sanka, wannan ita ce babbar nasara. Daga kauye har birni ba wanda bai sanni ba, ai kuwa shi ne babbar nasara. Suna da yawa in na ce zan zauna nai ta fada, za mu iya gama wannan hirar ba tare da na gama fadar su ba.

 

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da fim, tun daga farkon farawarki zuwa yanzu?

Ni wallahi idan na ce ga kalubale da na fuskanta game da fim gaskiya babu shi, in ba wannan kalubale na gabadayan mu ba, kamar yadda ake yi mana kallo, ana yi mana kudin goro, da tsohuwa da yarinya, in ma jaririya ce, ke ki ka zo Kannywood. Ki ka zo kina masana’antar nan cewa za a yi ke karuwace, wannan kalmar duk ita ta fi min ciwo. Wallahi idan za ka kwana kana zagina kana tsine min wallahi ko a jiki na, saboda na san ni ba tsinanniyar ba ce. Sannan in za ka kwana kana ce min karuwa ni ba ta damen ba, saboda ba ita ba ce. Amma da ake mana kudin goro gabadayan mu, har cewa ake yi dan fim ba shi da addini, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Ga ilimin addini a kawunan mu, sallar nan guda biyar ba ta wuce mu, ga tauhidi Allah ya ba mu, sannan ka ce dan fim ba shi da addini. Yanzu duk masu fadar hakan idan ka ce Allah ya isa, Allah fa zai isar maka. Ni ban da wannan ba abin da ya riske ni, lafiya lau nake cikin masana’antar.

 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa insha Allah


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

Next Post

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

Related

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
Nishadi

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

1 week ago
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

2 weeks ago
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
Nishadi

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

3 weeks ago
Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
Nishadi

Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

3 weeks ago
An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna
Nishadi

An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna

3 weeks ago
Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
Nishadi

Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ

4 weeks ago
Next Post
tusar gaba

Ko Kin San... Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al'adarsu?

LABARAI MASU NASABA

Kwale-kwale

Haɗarin Kwale-kwale Ya Ci Rayukan Mutane 15 A Zamfara

August 31, 2025
Sin Za Ta Kare Moriyarta Ta Hanyar Mayar Da Martani Game Da Sabon Matakin Kakaba Harajin Kwastan Da Amurka Ke Dauka

Trump Ya Kakaba Kashi 50 Kan Indiya Saboda Sayen Kaya Daga Rasha

August 31, 2025
An Lalata Tamfatsetsiyar Gonar Wiwi A Taraba Tare Da Kama Dan Shekaru 70 A Anambra 

An Lalata Tamfatsetsiyar Gonar Wiwi A Taraba Tare Da Kama Dan Shekaru 70 A Anambra 

August 31, 2025
Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

August 31, 2025
Yadda Kungiyoyin Firimiyar Ingila Suka Shirya Wa Kakar Bana

Yadda Kungiyoyin Firimiyar Ingila Suka Shirya Wa Kakar Bana

August 31, 2025
‘Yan Wasan Afirka Da Ake Ganin Za Su Yi Abin Kirki A Kakar Bana

‘Yan Wasan Afirka Da Ake Ganin Za Su Yi Abin Kirki A Kakar Bana

August 31, 2025
tusar gaba

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

August 31, 2025
Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

August 31, 2025
Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

August 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.