Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis.
Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin.
Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa yuan biliyan 640.8.
Daga cikin manyan kayayyaki, an samar da jimillar wayoyin salula biliyan 1.67 a shekarar 2024, karuwar kashi 7.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023. Kana, an kera kimanin wayoyin salular fasahar zamani biliyan 1.25, wanda ya karu da kashi 8.2 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)