Masana’antar raya al’adu ta kasar Sin, ta samu ci gaba bisa daidaito yayin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, wanda aka gudanar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
A cewar mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Lu Yingchuan, a shekarar 2024, darajar jimillar kadarorin sashen ta kai yuan tiriliyan 34.4, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.84.
Lu wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, ya ce tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin ta kuma cimma manyan nasarori a fannin bunkasa tasirin al’adunta.
Ya ce a shekarar ta 2024, jimillar adadin cinikayya a fannin al’adu na Sin ya kai yuan tiriliyan 1.4, inda karin abubuwan sayayya a fannin da suka kunshi wasanni, da zane mai motsi, da kayan wasan yara masu daraja ke kan gaba a samun karbuwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp