An bude sabuwar masana’antar samar da shimfidar layin dogo a lardin Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya, inda za ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da aikin layin dogo na sashen hakar ma’adanai wanda kamfanin kasar Sin na gina layin dogo (CRCC) yake aiwatarwa.
Kafa masana’antar ta nuna fara gudanar da aikin injiniya na layin dogon mai nisan kilomita 575 wanda zai hade sashen hakar ma’adanan karafa na Gara Djebilet da ke Tindouf da lardin Bechar.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Inganta Cibiyoyin Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara
- Roma Ta Sallami Kocinta Ivan Juric Bayan Wasanni 12 Kacal
A cewar Dong Lin, babban manajan reshen kamfanin CRCC dake Arewacin Afirka, masana’antar da aka kafa ita ce irin ta ta farko mai sarrafa ingantacciyar shimfidar layin dogo da wani kamfanin kasar Sin ya taba kafawa a yankin.
A yayin gudanar da aikin, CRCC ya aiwatar da tsarin zanen da aka yi da nufin inganta shimfidar layin dogon, da habaka karkonsa da kuma rage kudin gyaran da za a rika kashewa, in ji Dong
A lokacin da ake bikin bude masana’antar, Gwamnan Tindouf Mustapha Dahou ya nuna jin dadi da godiya a kan kokarin kamfanin CRCC da abokan kawancensa na cikin gida, inda hakan ya nuna irin gagarumar gudunmawar da suka bayar ga samun nasarar aikin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)