Sashin masana’antu a Nijeriya na fuskantar matsalolin ciki har da ma na tattalin arziki, inda masu gudanar da sashin suka kashe adadin naira Tiriliyan 1.11 wajen neman hanyoyinsamar da wutan lantarki a shekarar 2024, tare da sallamar adadin ma’aikata 17,949.
A cewar rahoton da kungiyar masana’antu a Nijeriya (MAN) ta fitar, ya nuna cewa an samu karin kaso 42.3 daga naira biliyan 781.68 da aka kashe kan wannan manufar a shekarar 2023.
- An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
Rahoton ya ce bangaren samar da abinci da abin sha sun kashe naira biliyan 229.41 a bangaren makamashi, sama da naira biliyan 182.76 a shekarar 2023, yayin da kudin makamashin sinadarai da magunguna ya rubanya zuwa naira biliyan 208.68.
Sashin ma’adinai da ba na karfe ba ta kashe kudin makamashi da kashi 33.7 zuwa naira biliyan 118.49, kuma masana’antar yadi, tufafi da takalmi kudin da ya kashe ya karu sau hudu, wanda ya kai naira biliyan 26.45 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 6.97 a shekarar 2023.
Rahoton ya ce duk da an samu karin wutar lantarki a cikin masana’antu a shekarar 2024, da adadin karin wuta na awa 13.3 a kwace ranar da ya karu daga awa 10.6 a shekarar 2023.
Kazalika karin kudin wuta ya karu da kaso 200 ga wadanda suke amfani da rukunin A, don haka kudaden da masana’antun ke kashewa wajen biyan kudin wuta nan ma ya karu sosai.
“A daidai lokacin da aka samu karin wutar lantarki, masana’antu da dama har yanzu suna fuskantar daukewar wuta a kai a kai, da tsadar wutan duk da kasar kuma ta fuskanci lalacewar babban layin wuta har sau 12, wanann shi ne babban abun damuwa.
“A neman mafita ga yawan daukewar wutar da karin farashin kudin mai da gas duk sun mamaye masana’antu,” rahoton ya shaida.
A daidai wannan gabar, adadin mutanen da suke barin aiki a kamfanoni ya karu daga 17,364 a 2023 zuwa 17,949 a shekarar 2024. A gefe guda kuma an samu sabbin ma’aikata 16,820 a 2024.
Dangane da saka hannun jari a fannin da ake samu, an ce fannin ya samu raguwar zuba jarin masana’antu da kashi 35.3 a duk shekara zuwa naira biliyan 658.81 a shekarar 2024, lamarin da ke nuni da rashin tabbas na tattalin arziki da kuma rage tsare-tsaren fadada ayyukan.
Rahoton ya kara da cewa, jimillar jarin ya ragu da kashi 11.3 zuwa naira tiriliyan 2.85, inda a bangaren filayen da gine-gine da kayan daki da sauran kayayyaki suka samu koma-baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp