• English
  • Business News
Sunday, August 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masani Habasha Ya Yi Karin Haske Kan Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Masani Habasha Ya Yi Karin Haske Kan Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

An kaddamar da wani sabon littafi jiya Asabar mai taken “Hadin gwiwar Afirka da Sin: Nazari kan Habasha” wanda ke nuna dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka daban-daban, mai cike da tarihi, musamman kan alakar dake tsakanin kasashen Sin da Habasha.

Littafin mai babi 7, sun yi karin haske kan fannonin da suka hada da manufar kasar Sin game da nahiyar Afirka, da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Habasha da Sin, da hadin gwiwar siyasa tsakanin Afirka da Sin.

  • Kasar Sin Ta Samu Girbin Hatsi Mai Armashi A Bana

Bugu da kari, littafin ya yi nazari kan nasarorin da aka cimma a dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a lokacin annobar COVID-19, da kuma nazari kan alakar dake tsakanin Sin da Afirka a karni na 21.

An kaddamar da littafin ne a gaban manyan jami’an gwamnatin Habasha, da jami’an diflomasiyyar kasar Sin dake kasar Habasha, da shugabanni da wakilan cibiyoyin nazari daban-daban, gami da masana da sauran su.

Marubucin littafin, Melaku Mulualem, wanda babban jami’i ne mai bincike kan huldar kasa da kasa da harkokin diflomasiyya a cibiyar kula da dabarun kasar Habasha, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka sun raya dangantaka mai dinbin tarihi cikin wadannan shekaru, wanda kuma ke kara habaka a ‘yan shekarun nan.

Labarai Masu Nasaba

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

Marubucin ya kuma tuna abubuwan da ya koya a jami’ar harkokin waje ta kasar Sin, a matsayin abin da ya ba shi kwarin gwiwa wajen rubuta littafin, wanda ya ce, ya nuna hakikanin hadin gwiwar samun nasara tare, a tsakanin kasashen Sin da Habasha. (Mai fassara: Ibrahim)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Wani Hamshakin Wata Ya Bayyana A Sararin Samaniyar Duniya

Next Post

Mutane 4 Sun Mutu A Wani Hadarin Mota A Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Related

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan
Daga Birnin Sin

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

24 hours ago
Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

1 day ago
Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 
Daga Birnin Sin

Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 

1 day ago
Kayayyakin Sin Sun Samu Karbuwa Yayin Bikin Nune-nunen Kayayyakin Abinci Na Afrika
Daga Birnin Sin

Kayayyakin Sin Sun Samu Karbuwa Yayin Bikin Nune-nunen Kayayyakin Abinci Na Afrika

1 day ago
Kasar Duniyar Wata Da Kasar Sin Ta Samo Ta Samar Da Sakamakon Nazari Fiye Da 150
Daga Birnin Sin

Kasar Duniyar Wata Da Kasar Sin Ta Samo Ta Samar Da Sakamakon Nazari Fiye Da 150

1 day ago
Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

2 days ago
Next Post
Mutane 4 Sun Mutu A Wani Hadarin Mota A Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Mutane 4 Sun Mutu A Wani Hadarin Mota A Hanyar Legas Zuwa Ibadan

LABARAI MASU NASABA

Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga ÆŠan’adam

Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga ÆŠan’adam

August 10, 2025
INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027

INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027

August 10, 2025
Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

August 10, 2025
Harin Ƴan Bindiga Ya Yi Sanadin Kashe Ɗansanda Da Wasu Mutane 4 A Kwara

Harin Ƴan Bindiga Ya Yi Sanadin Kashe Ɗansanda Da Wasu Mutane 4 A Kwara

August 10, 2025
Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

August 10, 2025
Yadda Jinkirin Tabbatar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Ke Cutar Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi

Yadda Jinkirin Tabbatar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Ke Cutar Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi

August 10, 2025
Gwamna Abba Ya Bai Wa Dalibai 1,130 Kayan Aikin Sana’o’in Hannu

Gwamna Abba Ya Bai Wa Dalibai 1,130 Kayan Aikin Sana’o’in Hannu

August 10, 2025
NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas 

NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas 

August 10, 2025
UADD Ta Yaba Wa Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Kan Himma Da Kishin Kasa 

UADD Ta Yaba Wa Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Kan Himma Da Kishin Kasa 

August 10, 2025
ADC Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM A Neja

An Maka Gwamnatin Neja Da NBC A Kotu Kan Barazanar Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM

August 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.