Shahararren masanin ilimin physics dan asalin kasar Sin, wanda kuma ya taba lashe lambar yabo ta Nobel Chen Ning Yang, ya rasu a yau Asabar a birnin Beijing yana da shekaru 103.
An haifi Yang a Hefei dake gabashin kasar Sin a shekarar 1922. Kuma cikin shekarun 1940, ya yi karatu a Amurka tare da koyarwa. A shekarar 1957 ya lashe lambar karramawa ta kwararrun masana ta Nobel a fannin ilimin physics.
Bayani game da muhimmin fanni a ilimin da ya kware cikinsa, wanda aka yiwa lakabi da “Yang-Mills gauge theory”, wanda Yang da Robert Mills suka fitar, na cikin muhimman binciken physics da suka yi tasiri cikin karni na 20.
Bayan dawowarsa kasar Sin, Yang ya ci gaba da koyarwa a jami’ar Tsinghua, inda cikin sama da shekaru 20 ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen kyankyashe, da horar da sabbin masu hazaka, da yayata musayar ilimi tsakanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)