Masanin kasar Switzerland Christophe Ballif ya bayyana a kwanakin baya cewa, kasar Sin ta kasance a matsayin gaba a fannin makamashin hasken rana a duniya, kasar Sin ta zuba jari da samar da sabbin makamashi, wanda ya taimakawa kasashe da dama wajen yin amfani da fasahohi ba tare da gurbata muhalli ba, ta hakan an nuna goyon baya ga kasashen duniya wajen kyautata tsarin sha’anin makamashi.
Farfessa Ballif wanda ya zo daga kwalejin nazarin fasahohin masana’antu na Lausanne na kasar Switzerland, ya bayyanawa ‘yan jarida na kasarsa a kwanakin baya cewa, sha’anin masana’antu masu amfani da makamashin hasken rana zai zama muhimmin makamashin da aka samar da wutar lantarki a wannan karni, kasar Sin ta bunkasa wannan sha’ani cikin sauri, wadda ta iya samar da batirin makamashin hasken rana, da kuma batura da aka yi amfani da su a cikin mota da sauransu, sha’anin zai iya samar da gudummawa ga duk duniya wajen kyautata tsarin sha’anin makamashi.
Farfessa Ballif ya kara da cewa, kasar Sin ta samar da muhimmiyar gudummawa ga duniya a fannin sha’anin samar da sabbin makamashi, wanda zai sa kaimi ga kasashe da dama da su yi amfani da makamashi mai tsabta, wannan labari ne mai kyau ga duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)