A kokarin ta wajen ayyukan jinkai a fadin duniya, Cibiyar ayyukan Jinkai ta Sarki Salman (KSrelief) na Masarautar Saudiyya ta ‘Saudi Noor’ ta kaddamar da aikin bayar da magunguna kyauta ga dubban masu fama da matsalolin ido daban-daban a garin Potiskum, shalkwatar karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe.
A yayin da yake karin haske ga manema labarai a Asibitin Kwararru da ke Potiskum, jami’in hulda da jama’a na cibiyar, Mohammad Al-Sahabi, ya ce an tsara aiwatar da shirin bayar da magungunan ne daga ranar 12 zuwa 19 ga wannan watan na Mayu, 2025, wanda ya kunshi manufar samar da cikakken aikin jinkai ga al’ummar da ke fama da matsalolin idanu a Arewa Maso Gabashin Nijeriya.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m
- Bam Ya Hallaka Ma’aikatan Hukumar Ilimi 2 A Hanyar Damboa-Maiduguri
Al-Sahabi ya kara da cewa, shirin ya kunshi ayyukan jinkai ta fannin matsalolin ido daban-daban wadanda suka hada da aiwatar da gwaje-gwajen idanu, cire yanar ido tare da bayar da tabarau na ido ga wadanda suka dace, don magance gazawar hangen nesa, da makamantan su.
Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman.
Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan dake addabar al’umma masu karamin karfi.
Ya ce, “tun lokacin da cibiyar ta fara ayyukan jinkai don yaki da cutar makanta a Nijeriya, cikin watan Oktobar 2019, KSrelief ta gudanar da gwaje-gwajen idanu sama da 218,000, da gudanar da tiyatar idanu sama da 21,000, kuma da bayar da tallafin tabarau sama da 45,000 ga al’umma.
“KSrelief ta samu karbuwa a matsayin daya daga cikin cibiyoyin jinkai a fadin duniya. Sannan kuma tun bayan kafuwar cibiyar a 2015, ta aiwatar da ayyukan jinkai sama da 3,400 a cikin kasashe sama da 107.
“Wanda a halin yanzu, ta na gudanar da ayyukan jinkan kiwon lafiya a kasashe sama da 30, musamman wajen yaki da makanta a Sudan, Yemen, Bangladesh, Mauritania, Nijeriya da sauransu.”
Ya kara da cewa, wadannan ayyukan jinkai su na tafiya kafada da kafada da manufofin kiwon lafiya na duniya tare da na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), a fafutikar samar da lafiyar idanu ga kowa a duniya.
Wasu da dama wadanda suka ci gajiyar tallafin a Asibitin Kwararru na Potiskum sun bayyana cewa, “Wannan babban taimako ne mai muhimmanci a rayuwarmu, muna godiya ga Masarautar Saudiyya dangane da wannan tallafin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp