Umar Abdullahi Hafizi, ɗalibai mai karatun Sociology a matakin shekara ta uku a Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya rasa ransa bayan da wasu da ake zargin masu ƙwacen waya ne suka kai masa hari a gidansa da ke unguwar Dorayi, a Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Talata.
- Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
- Jama’a Suke Tona Asirin Gurɓatattun Jami’anmu – Kwamishinan ‘Yansandan Kano
Rahotanni sun ce maharan sun soka masa wuƙa sannan suka gudu da wayarsa.
Umar ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya samu.
Jami’ar BUK ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar.
“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a kama waɗanda suka aikata wannan laifi.
An binne marigayin a garinsu da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Jami’ar ta buƙaci ɗalibai su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a tare da su.
Haka kuma ta roƙi jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen gudanar da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp