A yau Litinin, alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, watau MIIT sun nuna cewa, a karshen watan Nuwamba, yawan masu amfani da wayoyin salula na fasahar 5G a kasar Sin sun kai biliyan 1.002, wanda hakan ya zama wani muhimmin ci gaba da aka samu a kasuwar sadarwa ta duniya.
Wannan adadi ya nuna kashi 56 cikin dari na daukacin wayoyin salula da aka saya a kasar, kuma har ila yau ya nuna an samu karuwar kashi 9.4 cikin dari, idan aka kwatanta da na karshen bara. An samu bunkasar sayen fasahar 5G cikin hanzari ce bisa babban ci gaban da aka samar na ababen more rayuwa.
- Yankunan Arewacin Kasar Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Kare Filayen Noma
- Rushewar Gini Ya Kashe Rayuka 4, An Ceto Mutane 105 A Abuja A 2024 – FEMD
Alkaluman ma’aikatar ta MIIT sun nuna kasar Sin ta samar da tasoshin fasahar 5G kimanin miliyan 4.2 a karshen watan jiya.
A farkon bana dai, alkaluman masana’antu sun nuna cewa, tasoshin 5G na kasar Sin, da suka kasance manyan wuraren sada wayoyi da intanet, sun kai fiye da kashi 60 cikin dari na daukacin adadin wadanda suke kasashen duniya baki daya, wanda yake nuna matsayin kasar na zama a kan gaba wajen samar da fasahar 5G a duniya kaf. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)