‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban malamin addinin musulunci a sansanin Asolo da ke yankin Uso a karamar hukumar Owo da ke jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Oyinlade a ranar Asabar.Â
An nakalto cewa malamin yana tsaka da aiki a gonarsa ne daban suka sace shi zuwa wani wajen da ba a ba a sani ba.
Daya daga cikin iyalan malamin ya ce masu garkuwa sun tuntubesu amma ba su fadi adadin kudin fansa da suke bukata ba.
Ya ce sun Kai rahoton faruwar lamarin ga caji ofis din ‘yansanda da ke Uso.
Da take magana kan wannan lamarin, jami’ar watsa labarai na rundunar ‘yansandan jihar, Mrs Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa jami’ansu suna kan kokarin ceto malamin.