‘Yan bindiga sun sace tsohon Sakatare-Janar na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFA), Ahmed Sani Toro.
Toro, an ruwaito cewa an sace shi ne da dare a kan hanyar Abuja zuwa Jos tare da tsohon mataimakin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets Garba Iliya.
- Soyayya Mai Karfi: Tsaraba Ta Musamman Ta Ranar Mahaifi Da Masanin Fasaha Han Meilin Ya Samar
- Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri
Duk su biyun an yi garkuwa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Bauchi bayan sun je Abuja a ranar Juma’a daurin auren dan tsohon shugaban kungiyar wasa ta NFF, Alhaji Aminu Maigari.
Wani mai ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a Jihar Bauchi kuma aboki ga Toro ya ce, wadanda suka sace su har yanzu ba su tuntubi iyalan Toro ba.
A cewarsa, da gaske ne an sace su kusa da garin Ryom da ke a Jihar Filato a kan hanyarsu ta dawo Jihar Bauchi, inda ya kara da cewa, an sace su ne bayan sun je daurin auren dan Alhaji Aminu Maigari, da aka dura a babban masallacin Abuja a ranar Juma’a.