ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

by Sulaiman and Ibrahim Sabo
4 years ago
Wayoyin hannu

Wannan rubutu na yi shi ne saboda korafe-korafen jama’a masu ta’ammuli da na’urorin Kwamfuta da manyan wayoyin hannu da kullum ake amfani da su domin gudanar da al’amuran yau da kullum.

Ta’ammuli da Kwamfuta ko wayar hannu ya zamo jigo a rayuwar jama’a domin gudanar da aiyukan yau da kullum, kama daga kasuwanci, fannin ilimi, fannin lafiya, bincike-bincike, fannin tsaro, ayyukan kotu, fannin yada labarai da sauran al’amura masu yawan gaske.
Ilimin sarrafa kwamfuta da wayar hannu ya zama mai saukin gaske. Ganin yadda ake ta kara inganta su da kuma saukaka fahimtar yadda za’a sarrafa su ko da mutum ba shi da ilimin zamani a halin yanzu, za a ga kusan kowa yana da wayar hannu ko kwamfuta koma dukkansu biyu, babu babba babu yaro.

  • Babu Maganar Janye Wa Ahmed Lawan Takara — Hon. Bashir Machina

Yawaitar amfani da na’urori domin bukatun yau da kullum, yana da alaka da saukin mallakarsu, ko da yake masu iya magana sunce, iya kudinka iya shagalinka.

ADVERTISEMENT

Dukkanin wadannan na’urori sun yi tarayya wajen abubuwa kamar haka; saurin sarrafa aiki, rumbun adana abubuwa ko kayan da aka sarrafa, ababen dogaro lokacin gudanar da aiki, saukin dauka ko rikewa a hannu lokacin zirga-zirga da sauran al’amura.

Idan ba a samu abubuwa biyu zuwa uku daga cikin wadancan siffofi da na bayyana ba, yakan haifar da damuwa wajen sarrafa na’ura. Kwamfuta da wayar hannu sukanyi nauyi ko jinkiri wajen sarrafa aiyuka, saboda dalilai masu yawa. Amma zan yi bayani a kan wadanda suka fi muhimmanci.

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

Akwai cutar na’ura mai yaduwa (Birus), sanin kowane cutar na’ura ta bairos da ire-irensu suna taka rawa wajen sauya akalar sarrafa na’ura, sukan cutar da ita, suna hana ta yin aiki kamar yadda aka tsara ta, sai taki gaba taki baya. Amfani da manhajar maganceta (anti-virus) yana da matukar muhimmanci.

Wasu sukan cunkushe na’ura da manhajoji ba bisa ka’ida ba. Akwai wadanda suke akidar saka manhajoji iri-iri masu yawa ko da basu iya aiki da su ba. Yin hakan yana haddasa cunkushewar rumbun adana aiki (memory). Saboda cire manhajar da ba’a amfani da ita yana bunkasa aikin na’ura cikin sauri.

Yin amfani da na’ura a cikin yanayi mai zafi ko waje maras isashshiyar iska yana haddasawa sassan ita na’urar jinkirin aiki. Wanda hakan yana jawo koma baya ga ingancin na’ura. Dan haka idan babu na’urar sanyaya daki sai a kunna fanka, idan ita ma babu to sai a bude kofofi da wunduna domin iska ta dinga ratsa su a lokacin da ake aiki.

Idan ba a sabunta manhajoji a kan lokaci, to wannan ma babban al’amari ne da yake jawo tarnaki ga na’ura. Sabunta manhaja (update) a kan lokaci yana da amfani domin yana magance duk wata matsala tattare da ita kanta manhajar da sauran sassan na’ura dake aiki da manhaja lokacin gudanar da aiki.

Yin amfani da gurbatattun manhajoji (applications) na da illa ga na’ura. Domin yakan yi sanadiyyar bude dukkan kofofin sirri na na’ura domin cututtuka masu yawa su shiga. Kuma sukan zamo makamai da masu kutse ke amfani dasu wajen cutar da al’umma. Kuma an fi samun su a manhajoji na kyauta (free). Amfani da sahihan manhajoji shi ne mafi da cewa ga jama’a.

Barin datti ko kura a cikin na’ura, wato rashin tsaftace na’ura ko dakunan da ake amfani da ita, harma da teburin da aka dorata idan ta girke ce (desktop), yana da matukar illa wajen toshe kofofin shakar iska ga ita na’urar, har ma lalacewar wasu sassa saboda tsabar datti da kura. Saboda haka kula da tsaftar na’ura yana inganta sassanta yadda za ta yi aiki cikin sauki.

Fuskantar katsewar wutar lantarki a lokacin da ake tsakiyar aiki da na’uara, ko kwamfuta ta mutu saboda batir babu isashshen caji, babbar matsalace. Hakan yana haddasa matsala ga rumbun adana aiki (Hard Disk Dribe) kuma yana haddasa jinkiri wajen gudanar da aiyuka. Amfani da na’urar adana wutar lantar ki (UPS) da kuma isashshen caji ga wayoyi ko kwamfuta Laptop, zai taimaka kwarai. Ana so idan an dauke wuta sai a kashe a hakura har sai an sami wuta ko kuma a tayar da Janareto.

Wayoyin hannu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS
  • Sulaiman
    Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)
  • Sulaiman
    Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
Wayoyin hannu
Ibrahim Sabo
+ posts Bio
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (II)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Mene Ne Tsarin 5G?
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Yadda Ake Sarrafa Rubutu Ta Word-Processing

MASU ALAKA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya
Rahotonni

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

October 20, 2026
Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Next Post
Abubuwa 5 Da Zaku So Sani Game Da Biodun Sabon Gwamnan Ekiti Mai Jiran Gado

Abubuwa 5 Da Zaku So Sani Game Da Biodun Sabon Gwamnan Ekiti Mai Jiran Gado

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.