Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da ake yi wa lakabi da ‘Sai Masu Gida’ sun zura kwallaye har 4 a ragar Enugu Rangers a jihar Enugu.
Pillars wadda ta bakunci birnin Enugu domin fafata wasan mako na 7 tsakaninta da masu masaukin baki, ta zura dukkan kwallaye hudun a mintuna 45 na farkon wasan.
- Shugaba Xi Ya Yi Rangadi A Birnin Zhangzhou Na Lardin Fujian
- Fashewar Tankar Mai Ta Yi Ajalin Mutune, Ta Jikkata 300 A Jigawa
Ahmed musa ne gwarzon dan wasa a wasan bayan ya janyo bugun daga kai sai mai tsaron raga har sau biyu ya taimaka aka ci daya yayinda ya zura kwallo daya a raga.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Enugu Rangers su ka zage damtse domin rama kwallayen da aka zura masu, amma hakan bai yiwuwa ba duk da dai kadan ya rage domin kuwa Isaac Saviour kadai ya zura wa Pillars kwallo uku a ragarta.
Da wannan nasara da Pillars su ka samu ya sa ta koma matsayi na 4 akan teburin gasar Firimiyar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp