Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi bayyana cewa, masu kaiwa ‘yan bindiga bayanan sirri da ke kai hare -hare a cikin yankunan Bauchi sun fi ‘yan bindigar illa.
Bala ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga al’umar Gajin-Duguri da ke yankin mahaifarsa a karamar hukumar Alkaleri.
- Cire Tallafin Mai: Gwamnan Bauchi Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Rage Radadi
- An Yi Nasarar Ceto Mutum 30 Da Aka Sace Su A Jihar Bauchi
Ya kai ziyarr ne bayan tawagar jami’an tsaro sun ceto mutum 33 da ‘yan bindigar suka sace.
Kazalika, Bala ya sheda musu cewa, gwamnatinsa na kan yin aiki da hukomomin tsaro don tura jami’an sirri na farin kaya zuwa cikin kauyukan don su cafko masu hada baki da ‘yan bindigar.
A cewarsa, masu kaiwa ‘yan bindigar bayanan sirrin sun fi illa fiye da ‘yan bindigar, inda ya ce, ba za mu rungume hannayenmu don mu bar wasu ‘yan tsiraru su kore mu daga kasar da muka gada daga gun iyayen da kakanni ba.
Bala ya ce, mun gwammace mu sadaukar da kanmu don mu tabbatar da mun kare kanmu daga hara-haren ‘yan ta’adda.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, wadanda ‘yan bindigar suka sace da aka ceto sun hada da mata da yara kanana.