Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, ya ƙaryata iƙirarin shugaban Amurka, Donald Trump, cewa ana kashe Kiristoci a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Soludo ya ce tashin hankalin da ke faruwa a yankin ba shi da alaƙa da addini, domin mafi yawan masu kai hare-haren da waɗanda abin ya shafa Kiristoci ne.
- An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
 - Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
 
“Mutane ne ke kashe junansu, Kiristoci suna kashe Kiristoci,” in ji shi, inda ya bayyana cewa kusan kashi 95 cikin ɗari na mutanen yankin Kiristoci ne.
Ya bayyana cewa matsalolin siyasa, zamantakewa da tattalin arziƙi ne suka haifar da rikicin, ba bambancin addini ba.
Soludo, ya kuma shawarci gwamnatin Amurka da ta binciki gaskiya kafin ta yi magana game da Nijeriya, yana mai cewa irin waɗannan kalamai na iya ƙara tayar da hankali.
Ya ce matsalolin Nijeriya suna buƙatar yin nazari, ba kalaman da za su ɓata lamarin ba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma a Kudu maso Gabas da su haɗa kai domin samun zaman lafiya da sulhu.
A cewarsa, tattaunawa, adalci da kyakkyawan shugabanci su ne hanyoyin da za su kawo ƙarshen tashin hankali da dawo da amincewa tsakanin jama’a.
			




							








